Daga BASHIR ISAH
Ana fargabar wasu jami’an tsaro Civil Defence Corps (NSCDC) sun riga mu gidan gaskiya sakamakon kwanton ɓauna da wasu ‘yan bindiga suna yi musu a ƙauyen Bakana, Jihar Rivers.
Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana wa majiyarmu cewar wannan ɗanyen aikin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a.
Majiyar ta ce an bindige jami’an ne a Rafin Bakana cikin Ƙaramar Bukumar Degema.
“Biyu daga cikin jami’an da lamarin ya shafa Musulmi ne, kuma tuni aka yi musu jana’iza kamar yadda Musulunci ya tanada,” in ji majiyar.
Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewa, da aka nemi jin ta bakinsa, Mai magana da yawun NSCDC a Jihar Rivers, DSC Olufemi Ayodele, bai tabbatar da aukuwar hakan ba, haka kuma bai musa ba.
Sai dai, ya ce rundunarsu za ta yi magana nan gaba bayan samun ƙarin bayanai kan batun.
