Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana rashin fitaccen ɗan kasuwa Alhaji Aminu Ɗantata da cewa ba rashi ba ne ga al’ummar jihar Kano ko Arewa ko Nijeriya kaɗai ba, rashi ne da aka yi wa duniya.
Shugaban Kamfanin Hamir Global ɓentures, Alhaji Hamisu Rabiu Jingau ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Marigayi Alhaji Aminu ɗantata a Unguwar ƙoƙi.
Ya ce saboda Alhaji Aminu ɗantata uba ne kuma jagora ne ga dukkan al’umma musamman su ‘yan kasuwa haƙiƙa sun yi babban rashi na wannan bawan Allah sai dai kuɗin babu wani abu da za su faɗa sai dai su yi masa addu’a da jaje ga ‘yan’uwa da iyalai da abokan arziƙi da fatan Allah ya jiƙansa ya gafarta masa.
Alhaji Hamisu Rabiu Jingau ya ce su ‘yan kasuwa ba su da wani jagora da suka sa a gaba lokacin da yake raye sama da Alhaji Aminu ɗantata dukkan matsalolinsu da suka taso wanda suka fi ƙarfinsu su kan zo gabansa su gaya masa kuma ba su taɓa zuwa a iya saninsa da wata matsala ba wacce bai sauransu ya yi musu maganin ta ba, abubuwa sun faru ya shige musu gaba suna fata Allah ya yi masa rahama.
