Yadda tsohon ministan Buhari, Hadi Sirika ya raba wa ‘yar sa da ɗan uwansa kwangilolin biliyoyin kuɗi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A wani shaida a ranar Talata ya shaida wa babbar kotun da ke Abuja yadda tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, kaucewa bin doka wajen rarraba gwangiloli ga kamfanonin da ake zargin na iyalansa ne.

Mai ba da shaidar Adekunle Odofin, wanda jami’in hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ne, ya ce ba rarraba kwangilar ya taimaka wa Sirika ta yadda ya samu amincewar hukumar samar da kayayyakin gwamnati da majalisar gudanarwar Nijeriya.

Ya ce wannan na cikin abin da ake zargin Sirika da shi da iyalansa waɗanda ya tabbatar da cewa an biya kamfanoninsu kuɗin kwangilarsu kaso 100% a maimakon kafin alƙalami da ake bayarwa.

Mista Odofin, wanda shi ne shaida ta 12 da aka gabatar wa kotu a ranar Litinin, wanda ya ba da shaida kan kwangilar wacce za a ƙara girman ginin filin jirgin Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina. Sirika, ya riƙe muƙamin minista ne daga shekarar 2015 zuwa 2023, kuma garinsu ɗaya da shugaban ƙasa na lokacin Muhammadu Buhari, wanda shi ne ya naɗa shi.

A cewar mai ba da shaidar, Sirika ya raba kwangilar ce zuwa gida biyu, inda ya ba da ginin faɗaɗa masauƙin masu tafiya na filin jirgin ga kamfanin Enginos, wanda na ɗan uwansa ne mai suna Hamad Sirika, da da faɗaɗa filin ajiye jiragen sama ga kamfanin Al Buraƙ Global Inɓestment Limited waɗanda ‘yar ministan da mijinta suke da hannun jari a ciki. kamar yadda jami’in bincike a hukumar EFCC Mista Odofin ya bayyana.

Don haka, EFCC na zargin Sirika da ‘yarsa Fatima Sirika da mijinta, Jalal Hamma da kamfanin ma’auratan, Al Buraƙ Global Inɓestment, da zarge-zarge guda 6 na damfara da ta kai Naira biliyan 2.8.

EFCC ta bayyana cewa Ma’auratan sun samu kwangilar ma’aikatar sufurin ta biliyoyin kuɗi saboda mahifin Fatima shi ne shugaban hukumar.

Sannan hukumar na zargin Sirika da amfani da ofishinsa ba bisa ƙa’ida ba wajen ba da kwangila wacce ‘yarsa da mijinta suka mallaka.

Haka kuma tana zargin Sirika da amfani da ƙarfinsa wajen bai wa Al Buraƙ Global Inɓestment Limited kwangilar Naira biliyan 1.5 don faɗaɗa wurin ajiye jiragen sama.

Ta ce wannan kamfani ta bayan fage da Fatima da mijinta suka mallaka wanda take zargi yana da hannu a cikinsa inda ta alaƙanta Naira biliyan 1.3 da Sirika a matsayin ‘Kudin alherin ofis’ wanda EFCC ta ce ya saɓa wa sashe na 12 na kundin dokokin hukumar yaƙi da cin hanci da makamantan laifuka (ICPC).

Sai dai dukkan waɗanda ake zargi sun musunta zargin da ake yi musu.

Mai ba da shaidar ya ce, Sirika ya yi wannan dabara ta raba kwangilolin ne zuwa ƙanana-ƙanana domin samun amincewar ƙaramin jami’in gwamnati mai kula da ayyukan gwamnati da gujewa cure ayyukan da ka iya tilasta hukumomi masu zaman kansu su shigo domin duba aikin.

Sannan kusan laifi ne da ka iya saɓawa yarjejeniyar kwangila a bai wa ɗan kwangila kuɗin aikinsa 100% a matsayin kafin alƙalami. Tsarin shi ne biyan ɗan kwangila kuɗi a matakin kowanne aiki da ya gama har ya kammala.

A yayin da yake ba da dalili game da biyan kuɗin da aka yi wa ‘yan kwangilar, tsohon daraktan sashen samar da kayayyaki na hukumar sufuri ta ƙasa, Musa Odiniyan, a watan Janairu, ya ce, an yi haka ne domin aikin ya yi sauri domin shugaba Buhari ya ƙaddamar da shi kafin ya bar ofishinsa.

Mista Odiniyan ya kuma ba da shaida kan kamfanin Al Buraƙ bai cancanci kuma da ba zai ma kai ga samun kwangilar ba idan da an bi tsarin na adalci wajen neman ‘yan kwangilar.

Tsohon shugaban ƙasa, Buhari ya bar mulki ne a ranar 29 ga Mayun, 2023.

A zaman kotun ranar Talata, mai ba da shaidar ya bayyana wa kotun cewa an biya Naira miliyan 182 daga cikin kuɗin kwangilar zuwa asusun Zenith na Hamma, sai kuma Naira miliyan 110 da za a ba shi.

Sannan mai ba da shaidar ya ce, an saka wa Fatima a asusunta na Jaiz Bank Naira miliyan 7.4 a yayin da aka tura Naira miliyan 8.2 asusun banki biyu na Accesss – Naira miliyan 5.5 da Naira 2.7.

Haka kuma an tura wa kamfanin Trimark Engineering Serɓices Limited Naira miliyan 500 wanda aka yi amfani da su wajen faɗaɗa wurin ajiye jiragen sama. Sai dai ya ce an yi amfani da wannan kuɗi ne wajen yin wasu ayyuka daban da aka bai wa kamfanin.

Odofin ya ƙara da cewa akwai Naira miliyan 549 a asusun Al Buraƙ kuma har yanzu ba a kammala kwangilar ba.

Lauyan hukumar EFCC, Rotimi Jacobs (SAN), ya nemi a ba shi izinin gabatar da jawabin da su ma’auratan suka bai wa hukumar a lokacin da take musu tambayoyi a shekarar da ta gabata a matsayin hujja.

Sai dai lauya mai kare waɗanda ake ƙara ya soki buƙatar yana mai cewa hujjoji ne da aka samu a lokacin da aka tilasta wa mutanen biyu.

Alƙalin kotun, Slyɓannus Oriji, ya yanke hukuncin cewa ya yi wuri kotun ta iya tantance ko jawabin zai iya zama na amsa laifi.

Daga nan ya ba da umarnin gudanar da wata ƙwarya-ƙwarya shari’a domin tabbatar da yanayin da aka ba da jawabin domin gane babu tilastawa a cikinta.

Mai shari’ar ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 27 da 28 da 29 ga watan Oktoba.

Mista Odofin, wanda shi ne shaida 12 ya fara ba da shaidar ne da ba da labarin yadda ƙararraki da ma’aikatan hukumar sufurin jiragen saman ya sa EFCC fara bincike kan Sirika da waɗanda ake zargin.

Sannan EFCC ta bayyana cewa bayan binciken, ta samu takardu da ke ɗauke da rubutun Sirika inda ya raba kwangilar a tsakanin kamfanonin Enginos Nigeria Limited da Al Buraƙ.

Ya shaida wa kotun cewa wasu jami’an bincike sun duba motar Okorie a lokacin da ya zo ofishin hukumar domin amsa tambayoyi kan inda suka samu wani littafi ɗauke da rubutun “ragowar ayyukan 2021”.

Sannan shaidar ya ce, “A jerin ayyukan a daidai na 13 sun ga bayanin wani kwangilda na ginin wurin masaukin matafiya da faɗaɗa wurin ajiye jiragen sama a Kaduna.

Kuma a kan wannan aikin, akwai jan biro da ke nuna an tsaga aikin zuwa gida biyu.

An nuna wa Sirika rubutun wanda EFCC ke kyautata zaton rubutunsa ne, amma ya musanta hakan cewa bai taɓa rubuta hakan ba.

Daga nan ne Mista Odofin ya tabbatar da cewa sun ɗauki samfurin rubutunsa inda suka kai ziyara hukumar tare da samun wasu takardu da rubutun hannun ya yi daidai da na Sirika.

Ya ce sun tura takardun ne wajen ƙwararru da rubutun da ake magana a kai wanda ministan ya ya musanta da takadun da suka samo a ofishin hukumar.

Sakamakon ƙwararrun da suka bayar a ranar 14 ga Mayun 2024, ya nuna rubutun biyu duk na mutum ɗaya ne wato Sirika.

Sannan hukumar ta gayyaci Sabo Yahaya, wanda shi ne shugaban kamfanin Tramak Engineering Serɓices Limited kan Naira miliyan 500 da aka tura wa kamfanin daga bankin Zenith Bank na kuɗin kwangilar suke yi wa Al Buraƙ Global Inɓestment.

Haka ita ma surukar Sirika, Saratu Chinade, an gayyace ta wacce ita ma tana da ikon sa hannu kan asusun bankin Zenith na Al Buraƙ.

A ranar 27 ga Yuni ne EFCC ta gabatar takardun aiki na Fatima da Hamma daga NNPC da hukumar kula da albarkatu da haƙo man fetru (NUPRC) da ke nuna sun samu aikin kwangilar ne a yayin da suke aikin gwamnati.

EFCC ta kuma nemi da a hukunta Sirika tare da ƙaninsa da kamfanin biyu kan zargin amfani da ofishinsa ba bisa ƙa’ida ba da zamba cikin aminci wajen ba da kwangilar da ta kai Naira biliyan 19.4.

By ukarofi