
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa a matsayin sabon shugaban gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars.
A sanarwar da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce naɗin wani ɓangare ne nq ƙoƙarin ƙarfafa ƙungiyar gabanin fara sabuwar kakar Premier Nijeriya.
Ya kuma ce, an naɗa Ahmed Musa ne, wanda ɗan wasan ƙungiyar ne, bayan tuntuɓar masu-ruwa-da-tsaki a harkokin wasanni a faɗin jihar.
A watan Octoban 2024 ne Kano Pillars ta sanar da ɗaukar kyaftin ɗin na ƴan tawagar Nijeriya domin buga mata wasanni Premier League ta Nijeriya.
Ahmed Musa shi ne ɗan wasan ya fi buga wa Super Eagles wasa inda ya ke da adadi guda 111, wanda kuma ya sake dawo wa Kanon Pillars a wani karo domin cigaba da bada gudumawarsa ga ci-gabanta.
