Martani ga Malam Asadussunnah: Hange mafi alkhairi

Daga TY SHABAN

Hakika akwai badakala iri-iri a cikin Masana’antar Kannywood, kamar yadda Malam Asadus Sunna ya bayyana a cikin wani faifen bidiyo mai taken ‘Illar Finafinan Hausa…’ Hakika na tabbata akwai kuma abubuwan ALKHAIRI a cikin wannan masana’anta ta Kannywood duk da cewa na ga Mallam Asadus Sunna ya gaza bayyana alkhairi ko da da kwayar zarra a cikin finafinan Hausa, wanda hakan rashin adalci ne da kawo gyara wurin sauya ba daidai ba da daidai.

Hakika kowace irin al’umma, wala-allah masana’antar Kannywood, cikin kasuwa, ma’aikata ta gwamnati ko masu zaman kansu, ba a rasa na kirki da bara gurbi. Don haka babu yadda za a yi wa Kannywood kudin goro da cewa, kowa da ke ciki mutumin banza ne ba tare da bambance  aya daga tsakuwa ba.

Akwai malaman addini da yawa da suka taba yabo ko shaida irin ayyukan alkhairi da ke jibi da adabi da ’yan Kannywood ke gudanar da kasuwancinsa tare da nuna misalin finafinan Hausa da wakoki.

A cikin watan azumin watan Ramadan da ya gabata, Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa (MOPPAN) reshen Jihar Kano ta shirya shan ruwa da  buda-baki, inda mashahurin malamin nan, Mallam Ibrahim Khalil, kuma Shugaban Majalisar Malaman Jihar Kano, ya gabatar da lakca mai taken ‘Mahangar Addinin Musulinci Akan Fim, Tasirinsa A Rayuwar Dan Adam.

Mallam ya ambaci irin alkhairan da ke cikin sana’ar fim kuma ya bayyana yadda ya kamata a gudunar da sana’ar daidai da tsarin zamantakewa da koyarwar addini. Ya yi yabo da jinjina akan wasu ayyukan Kannywood, wanda hakan ya ba wa masu shirya finafinai kwarin gwiwa da kawo gyara da samar da finafinai masu inganci da tasiri a rayuwar dan adam.

Na so a ce Malam Asadus Sunna ya kira kasidarsa da taken ‘Illar Finafinan Hausa ko Tasirinsu…’ Hakan zai ba shi damar fadin alkhairi ko sharrin da ke cikin sana’ar.

A karshe, Ina rokon Malam Asadus Sunna da ya yi wa Kannywood adalci wurin kawo  alkhairin Kannywood ko da kuwa bai taka kara ya karya ba tare da bayar da shawara akan hanyoyin da za a bi wurin kawo gyara da cigaba wurin samar da finafinan da za su yi daidai da addinin Musulunci da dabi’ar Hausawa.

Allah yasa mu dace.

TY Shaban, Jarumi ne kuma Mai Shiryawa a Kannywood.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *