Yau BBC Hausa za ta fara shirin ‘Mahangar Zamani’ a shafin YouTube

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Fitacciyar kafar yada labaran nan ta BBC Hausa za ta kaddamar da wani sabon shiri mai taken Mahangar Zamani yau Asabar, 2 ga Oktoba, 2021, a shafinta na YouTube, domin matasa da mata.

Sanarwar hakan ta fito ne a wata sanarwar manema labarai da BBC din ta aike wa Manhaja a Abuja jiya Juma’a, tana mai cewa, “Mahangar Zamani sabon shiri ne a YouTube daga ma’aikatan BBC Hausa, domin matasa da mata.

“Shirin wanda za a kaddamar da shiri a ranar 2 ga Oktoba mai tsawon minti 25 sau biyu a kowanne mako, zai mayar da hankali ne kan batutuwan da matasa masu tasowa suka fi bibiya da tattaunawa akai.

“Shirin, wanda Madina Maishanu za ta rika gabatarwa, zai rika duba kan al’amuran da ake tattaunawa kansu a kafafen sada zumunta da kuma ainihin kafafen yada labarai na asali.”

A yayin da Wakiliyar BBC Hausa, Madina Maishanu ke yin karin haske kan sabon shirin, ta ce, “gabatar da shirin Mahangar Zamani wani cikar buri ne a wajena. Na ji dadin yadda shirin zai rika zuwa har gare ku kuma ya bayar da dama wajen samar da mafita (ko warware matsala).”

Shi dai wannan sabon shiri na Mahangar Zamani da kafar yada labaran ta kirkiro za a rika saka shi ne a shafin BBC Hausa na YouTube da Facebook, domin masu sauraro su samu a lokacin da suke bukata.

Babban Editan Sashen Hausa na BBC, Malam Aliyu Tanko, ya ce, “makasudin gabatar da shirin shine, domin a bai wa matasa da mata wata muryar da ta dace da matsayarsu a al’ummar wannan zamani. Mu na so ne u bai wa masu bibiyar mu ’yantaccen tunani da hange da kuma damar ’yancin yin mukabala kan al’amura masu muhimmanci.”

Daga nan sanarwar ta kara da cewa, kashin farko na Mahangar Zamani zai tattauna kan batun dangantaka tsakanin malaman jami’a da dalibai ne, inda za a dubi batun illar da ke akwai tsakanin alakarsu kuma za a bai wa kowane bangaren ra’ayi damar bayyana fahimtarsa.

A kashi na biyu kuma za a tattauna batun mata a arewacin Nijeriya ne, inda a duba ikon da mata ke da shi a mahangar addini da yadda maza ke kaskanta su ta hanyar cin zarafinsu. Kana kuma za a ji ra’ayin mace da namiji a cikin kashin.

Za a fara saka shirin ne da musalin karfi 10:00 na safiyar yau Asabar, haka nan za a iya tattauna na batun da taken #MahangarZamani a kafafen sada zumuntar.