Gwamna Sule ya zira ƙwallo a raga a wasan bikin cikar Nasarawa shekara 25 da kafuwa

Daga BASHIR ISAH

A matsayin wani ɓangare na cikar Jihar Nasarawa shekara 25 da kafuwa, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abdullahi Sule, ta shirya wasan ƙwallon ƙafa na sada zumunta inda aka fafata tsakanin ɓangaren Gwamna Sule da ya ƙunshi tsoffin masu buga wa jihar wasa, da kuma ɓangaren tsoffin ‘yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙsa, wato Super Eagles.

Sanarwar da ta fito ta hannun jami’in yaɗa labarai na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nasarawa United, Eche Amos, ta nuna an buga wannan wasa ne a ranar Alhamis da ta gabata a babban filin wasannin motsa jiki da ke Lafia babban birni jihar.

Wasan wanda aka tashi kunnen doki (1-1) ya nishaɗantar da ‘yan kallo musamman ma ganin yadda Gwamna Sule ya riƙe matsayin kaftin na ɓangarensa.

Gwamna Sule shi ne ya zira ƙwallon da suka ci a raga bayan da aka ba shi damar bugun daga kai sai mai tsaron gida ko kuma fenariti, inda ya samu nasarar zira ƙwallo a ragar da Peter Rufai ke tsaronta.

Tsoffin ‘yan wasan Super Eagles da aka gani a wasan sun haɗa da Kanu Nwankwo da Daniel Amokachi wanda ke riƙe da matsayin SSA kan harkokin wasanni ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, sai kuma Tijjani Babangida da Dominic Iorfa da Austin Eguavoen da Ifeanyi Ekwueme da kuma Justice Christopher.

A ɓangaren Gwamna Sule kuwa akwai Moga Stephen da T.Y. Doma da Abu Scatter da Abba General Abdullahi da Vincent Christopher da Husseini Doma da Adamu Musa, sai kuma Michael Anyanya Anyanwu.

An ƙirƙiro Jihar Nasarawa ne a ranar 1 ga Oktoban 1996, ƙarƙashin gwamnatin Marigayi Janar Sani Abacha, wanda hakan ke nufin jihar ta cika shekara 25 ke nan da kafuwa.