02
Oct
Daga TY SHABAN Hakika akwai badakala iri-iri a cikin Masana'antar Kannywood, kamar yadda Malam Asadus Sunna ya bayyana a cikin wani faifen bidiyo mai taken ‘Illar Finafinan Hausa...’ Hakika na tabbata akwai kuma abubuwan ALKHAIRI a cikin wannan masana'anta ta Kannywood duk da cewa na ga Mallam Asadus Sunna ya gaza bayyana alkhairi ko da da kwayar zarra a cikin finafinan Hausa, wanda hakan rashin adalci ne da kawo gyara wurin sauya ba daidai ba da daidai. Hakika kowace irin al’umma, wala-allah masana'antar Kannywood, cikin kasuwa, ma'aikata ta gwamnati ko masu zaman kansu, ba a rasa na kirki da bara…