
Daga BELLO A. BABAJI
Mai martaba Sarkin Fika kuma Shugaban Majalisar Sarakunan gargajiya ta Jihar Yobe, Alhaji Dakta Muhammad Ibn Abali Muhammad (CON, CFR), ya umarci a sanar da ƙarin girma da naɗin wasu daga cikin muƙarrabansa.
Mutanen sune; Air Komodo Ibrahim Alƙali (rtd) daga Galadima zuwa Madakin Fika; sai Ali Adamu Fika wanda aka naɗa a matsayin Wazirin Fika; sannan Alhaji Ali Gimba Fika daga Sakataren riƙon ƙwarya zuwa Sakataren Majalisar Masarautar Fika.
Wata takarda da Sakataren masarautar, Ali Gimba Fika ya fitar a ranar 30 ga watan Disamba, 2024, ta ce tuni mutanen da aka naɗa suka kama aiki.
