Daga RABIU SANUSI a Kano
Daraktan mulki da Kuɗi na ƙaramar hukumar Tarauni Alhaji Abdulkadir Muhammad Arabu, tare da shugaban sassa na ƙaramar hukumar, Suleiman Umar sun kammala aikinsu a ranar Litinin na tsowon shekaru 35 in da daraktan mulki mai barin gado ya miƙa kujerar daraktan mulki ga ma’ajjin ƙaramar hukumar Tarauni kwamared Bello Hassan Durimin Zungura yayin da Suleiman Umar ya miƙa kujerar sa ta cpo ga shugaban ma’aikata Nazifi Bello.
Shima Nazifi Kuma ya miƙa kejarar ta shugaban ma’aikata ga Tijjani Muhammad Lawan sai Kuma ma’ajjin ƙaramar hukumar ya miƙa kujerar sa ga kashiyan ƙaramar hukumar Ahmed M Ahmed dukkanin su a matsayin riƙo.
Alhaji Abdulkadir Muhammad Arabu Wanda ya yi fice wajen gudanar da ayyukansa cikin ƙwazo, jajircewa, da kishin ci gaban al’umma da ciyar da ma’aikatan ƙaramar hukumar wanda hakan ya taimaka wajen bunƙasa ayyukan ƙaramar hukumar Tarauni.
A yayin bikin kammala aikin shi ya miƙa ragamar kujerarsa ga ma’ajjin Ƙaramar hukumar Tarauni kwamared Bello Hassan, a wani taro da aka gudanar a ofishin shugaban ƙaramar hukumar Tarauni.
Alh Abdulkadir Muhammad Arabu ya roƙi al’ummar ƙaramar hukumar Tarauni da ma’aikatan yankin da cewa duk wanda ya ɓatawa bisa kuskure ya yafemasa idan shi Kuma yace shi dai duk wanda ya ɓata masa ya yafe.
Alhaji Abdulkadir Muhammad Arabu da shugaban sassa Suleiman Umar sun godewa al’ummar ƙaramar hukumar da shugaban ƙaramar hukumar Ahmed Ibrahim Muhammad sekure bisa haɗin Kai da goyen baya da ya basu har suka kammala aikinsu lafiya.
A jawabinsa sabon daraktan riƙon na ƙaramar hukumar Tarauni kwamared Bello Hassan yayi alƙawarin yin aiki tuƙuru wajen Ƙara farfaɗo da aiyyukan ƙaramar hukumar Tarauni inda ya nemi haɗin Kai da goyen bayan ma’aikatan yankin da shugaban ƙaramar hukumar domin ya sauke nauyin da aka ɗaura masa.
Da yake jawabi shugaban ƙaramar hukumar Tarauni Alh Ahmed Ibrahim Muhammad sekure ya yabawa tsohon daraktan mulki mai barin gado Alh Abdulkadir Muhammad Arabu da shugaban sassa Suleiman Umar bisa yadda suka nuna jajircewar su wajan bashi dukkanin shawarwari a lokacin da ya kama aikin bayan zaɓen sa a shugabancin ƙaramar hukumar Tarauni.
Ahmed Ibrahim Muhammad sekure daga nan ya yi fatan Alkairi sabon daraktan mulki da Kuɗi na riƙo kwamared Bello Hassan a riƙon da zai yi.
