Mun hallaka ƴan bindiga 40 da kama masu aikata manyan laifuka 916 a 2024 – Kwamishinan ƴan sandan Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Kwamishinan ƴan sandan jihar Katsina, CP Aliyu Musa, ya ce jami’an rundunarsu sun kashe ƴan bindiga 40 acikin shekara guda.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewar, an kama masu aikata laifuka 916 tare da ceto mutane 319 da aka yi garkuwa da su a cikin lokacin.

Kwamishinan ya bayyana haka ne a ranar Litinin a lokacin da ya ke bayyana irin nasarorin da rundunar ta samu shekarar 2024.

“Ina so in tabbatar da jajircewar da aka yi na yaƙi da laifuka da rundunarmu ta yi cikin wannnan shekara, jajircewar da muka yi ta haifar da raguwar masu aikata laifuka a faɗin jihar.”

“Mun yi nasarar tarwatsa mashahuran dabar ‘yan bindiga da dama. Mun kuma bankaɗo bayanai masu yawa, mun kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su, yayin da muka yi nasarar gurfanar da masu aikata laifi da dama a gaban ƙuliya”, inji Kwamishinan.

“Ƙoƙarinmu ya ba da sakamako mai kyau, kuma muna alfahari da ci-gaban da muka samu.”

“Mun kashe ‘yan bindiga 40, tare da kawo tarnaƙi ga ayyukansu don al’ummominmu su kasance cikin aminci.”

“Mun ƙwato dabbobi 2,081 da aka sace, inda muka mayar da su ga masu su don bunƙasa tattalin arziƙin yankin.”

Kwamishinan ya cigaba da cewa, “Mun kama mutane 199 da ake zargin ’yan fashi da makami ne, inda muka kawar da su daga kan tituna don sama wa al’ummarmu tsaro.”

“Mun kuma gurfanar da wasu manyan dillalan miyagun ƙwayoyi guda 23 a gaban kotu, tare da kawo tarnaƙi ga safarar haramtattun kayayyaki don inganta rayukan al’umma mai aminci da lafiya.”

Haka kuma ya ce, “Mun samu nasarar kamawa tare da gurfanar da wasu mutane 32 da ake zargi da ɓartana kayan gwamnati ko na al’umma a gaban ƙuliya, inda muka tabbatar da cewa an gurfanar da waɗanda ke neman lalata dukiyar al’ummarmu.”

“Kazalika aikin da muka yi ya kai ga kama wasu mutane 89 da ake zargin ɓarayin motoci ne tare da ƙwato motoci da babura sama da 27, lamarin da ya sa hanyoyinmu suka samu tsaro ga kowa da kowa”, inji shi.

By Babaji