Zubairu Balannaji ya lashe gasar gajerun labarai ta Gwamnatin Jihar Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano ta ayyana Zubairu Musa Balannaji a matsayin wanda yazo na farko a gasar gajerun labarai ta shekarar 2024

Da take bayyana sakamakon gasar a ɗakin taro na Malam Aminu Kano dake Mumbayya, Dr. Halima Abdulkadir Dangambo Wanda shugaban kwamitin gasar Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ya yi bayani a madadin ta inda ya bayyana labarin ‘Bahaushiyar Al’ada’ wanda marubuci Zubairu Musa Balannaji ya rubuta a matsayin wanda ya yi nasara Kuma ya zama na farko cikin labarai 50 da suka fafata a cikin gasar.

Kazalika, ya bayyana labarin ‘Gadon gida saida Horo’ wanda Ɗanladi Haruna Zakariyya ya rubuta a matsayin wanda ya zo na biyu, sai labarin Hauwa Shehu Mai taken ‘Bahaushe Mai arziki ne’ a matsayin wanda yazo na uku cikin labarai 50 da suka fafata a gasar.

A nasa jawabin Shugaban hukumar Abba El-mustapha ya bayyana farin cikinsa kan yadda gasar ta gudana tare da taya wanda sukayi nasara murna.

Da yake jawabi Zubairu Musa Balannaji ya godewa Allah, tare da nuna farin cikin shi dangane da wannan gagarumar nasarar da labarinshi ya yi na zama na farko cikin tarin labaran da aka tantance a yayin gasar, ya kuma sadaukar da nasarar da ya samu ga mahaifinsa da ya rasu shekarar da ta gabata.

Hukumar ta bawa wanda yazo na farko kyautar Naira 500,000 sai na biyu Naira 300,000 a yayin da ta uku ta sami kyautar Naira 200,000.

By ukarofi