
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jihar Katsina ta samu rahoton samun masu ɗauke da cutar mashaƙo guda 1,000 tun daga Junairu, 2026, inda kuma kaso 5 na waɗanda abin ya shafa suka rasu, lamarin da ya tilasta wa gwamnatin jihar hanzarta ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile cigaba da yaɗuwar cutar.
Sakatariyar riƙo ta Hukumar kula da Lafiya a Matakin Farko (PHCA) ta jihar, Shaima’u Abba ce ta bayyana haka ga manema labarai a cibiyar aikin gaggawa na hukumar da ke garin Katsina a ranar Lahadi.
Ta bayyana mashaƙo (diphtheria) a matsayin cuta mafi haɗari da ake saurin kamuwa da ita wadda ke shafar maƙoshi, inda ta ce hakan babban abin damuwa ne yanzu acikin al’umma.
A cewarta, zuwa sati na 35 na aikin daƙile cutar a ranar 28 ga Agusta, an samu rahoton masu ɗauke da cutar a ƙananan hukumomi 29 na jihar, inda Funtua ce ke da mafi girman adadin, sai Kankia, Bakori, Katsina, Mashi sannan kuma Daura.
Shaima’u Abba ta kuma tabbatar da cewa, Gwamnatin Dikko Raɗɗa tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin an kawo ƙarshen cigaba da yaɗuwar cutar ta wasu shirye-shirye da ta ƙaddamar a ƙarƙashin jagorancin PHCA, Ma’aikatar Lafiya, Hukumar kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Cibiyar kula da Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) da sauran masu ruwa da tsaki.
Ts ƙara da cewa, tuni aka fara aikin sanya ido, tattara bayanan rahotanni da ɗaukar matakan kariya a sassan daban-daban na yankunan da annobar ta shafa a ƙarƙashin tsarin kula da ɓarkewar cuta.
Kazalika, ta yi kira ga iyaye da masu raino da su tabbatar da cewa yaransu sun karɓi dukkan rigakafin da ake bayarwa da kuma gaggauta garzayawa zuwa asibiti domin karɓar magani da zarar an ga alamar bushewar maƙogwaro, wahalar haɗiya ko numfashi, kumburin wuya ko kuma sauyawar kalar maƙoshi.
