Masu sayar da mai a garuruwan Abuja, Kogi da Nasarawa sun rufe gidajen mai dalilin shirin zanga-zanga da za gudanar ɗaya ga watan Agusta 2024, wanda ya jawo layin mai na dawowa a sassan garuruwan .
A birnin tarayya, gidajen mai da dama har wanda hukumar NNPC ta mallaka sun daina sayar da mai ranar Juma’a. Wanda hakan ya jawo gidajen man da ke sayarwa, layi yayi yawa sosai a anguwannin Dei-Dei, AYA, Zuba da sauransu.
Haka lamarin yake a garuruwan Legas, Ogun, Ibadan. Masu aikin tuƙa mota suna koka wa yadda hakan ba ya bari suyi aikin su sosai yadda yakamata.
