Ofishin jakadancin Amurka ya yi gargaɗi kan zanga-zangar gama-gari a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya yi gargaɗi game da zanga-zangar gama-gari da ake shirin yi a Nijeriya wanda ake tsammanin farawar sa daga 29 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Agusta.

Sanarwar ta wacce ta fito daga ofishin, ta ce zanga-zangar ka iya haifar da tare hanyoyi, madakatun bincike, cinkoson ababan hawa da artabu na gaba-da-gaba duk da cewa ba a san takamaiman wuraren da hakan za su faru ba.

Domin kaucewa faɗawa cikin haɗari, ofishin jakadancin ya bada shawarwari kamar haka; Bibiyar gidajen jaridu na gida domin samun labaru da ɗumi-ɗuminsu, nisantar tarurruka, sanin abubuwan da ke faruwa a wurare mafi kusa, nazari game da tsarin tsaro tare da barin wayoyi a kunne saboda ko-ta-kwana da kuma yin gabatarwa yadda ya dace.

Sannan, duk da yanayin da ake ciki na ɗar-ɗari, ofisoshin ayyukansu na Abuja da Legas za su cigaba da harkokinsu kamar yadda aka saba.

By Babaji