
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Yayin da ake cigaba da shirin zanga-zanga a faɗin Nijeriya, lauyan kare ƴancin Ɗan Adam, Inibehe Effiong ya aika da saƙo ga Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Kayode Egbetokun inda ya buƙaci a bai wa masu zanga-zangar kariya.
Effiong ya ce zanga-zangar lumana a dokar Nijeriya ta halatta, dan haka akwai buƙatar hukumomin tsaro su ba su kariya, ya na mai kafa hujja da sakin-layi na 39 da na 40 na kundin dokar ƙasa.
Ya ƙara da kira ga Sufetan, ya umarci dukkan kwamishinoni da ɓangarorin da ke da alhakin bayar da tsaro ga al’umma domin tabbatar da isasshen tsaron rayuka da dokiyoyin al’umma, yana mai cewa aikinsu shi ne su sauƙaƙe hanyoyin yi ba su tsananta ba kamar yadda ya ke a cikin dokokin ƙasa.
Ya ƙara da tunatar da Kayode dokar Ƴan sanda ta 2022 da ke wajabta bada kariya ga ƴancin Ɗan Adam, yana mai gargaɗin cewa duk wata tarzoma ko ƙoƙarin tauye haƙƙin masu zanga-zangar, hakan zai bayu zuwa ga hukuncin laifin sata, kamar yadda dokar hana cin-zali ta 2017 ta nuna.
