Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Nijeriya ta koka kan zanga-zangar wahala da tsadar rayuwa da aka shirya yi.
Matsayin Majalisar kan wannan batu yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a ƙarshen taron kwamitocin zartaswa na ƙungiyar da ta ke yi duk bayan wata uku.
Sanarwar wacce ta samu sa hannun Shugaban Kwamitin gudanarwa na Majalisar, Mai Martaba Sarki Alh. (Dr.) Yahaya Abubakar, CFR, Etsu Nupe, ya bayyana cewa taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin mai martaba Alhaji (Dr.) Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni, Sarkin Musulmi, da kuma Mai Martaba (Dr.) Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, CFR, Ojaja Il, Ooni na Ife.
Ya bayyana cewa taron buɗe ya samu halartar sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, CON, CFR, a matsayin babban baƙo. Har ila yau, mambobin kwamitin zartaswa da suka haɗa da dukkan shugabannin majalisar gargajiya na jihohi 36 na tarayya da na babban birnin tarayya (FCT) sun halarci taron.
Sanarwar ta ce, bayan kammala tattaunawa da ‘yan majalisar a yayin zaman da aka yi, majalisar ta lura kuma ta yanke hukunci kamar haka: “Majalisar ta yabawa gwamnatin tarayya bisa samar da tallafin kuɗi, tsarin rancen ɗalibai, kuma kwanan nan ta amince da mafi ƙaranci albashi na Naira 70,000.00 ga ma’aikatan Nijeriya.
“Ya kamata gwamnati ta rage tsadar rayuwa a kasar nan ta hanyar magance tsadar albarkatun man fetur, tsadar kuɗin wutar lantarki da kayan aikin gona.
“Mambobin Majalisar a yayin tattaunawar sun nuna rashin amincewa da ra’ayin da aka ce an yi na zanga-zangar taɓarɓarewar tattalin arziki. Tunanin ba shi da amfani kuma zai iya haifar da rushewar ayyukan tattalin arziki, tada zaune tsaye da asarar rayuka da dukiyoyi. Dangane da haka, muna ba da umarni ga kowa da kowa da su rungumi tattaunawa don nemo mafita ga matsalar.”
Majalisar ta bayyana cewa, majalisar ta lura da tsananin rashin aikin yi da kuma ƙalubalen tattalin arzikin da ‘yan ƙasa ke fuskanta, waɗanda ke haifar da tashe-tashen hankulan matasa da sauran matsalolin tsaro.
“Majalisar ta kuma lura da shirye-shiryen ƙarfafa matasa daban-daban na Gwamnatin Tarayya da na Jihohi.
Don haka majalisar ta yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su tabbatar da aiwatar da wadannan shirye-shirye da ake yabawa yadda ya kamata; tare da yin kira gare su da su tashi tsaye wajen aiwatar da tsare-tsare masu inganci na tattalin arziki da ke da nufin rage raɗaɗin talauci, samar da ababen more rayuwa da walwala, samar da ayyukan yi, tare da yaƙar cin hanci da rashawa a dukkan ɓangarorin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume wanda ya kasance babban baƙo a taron, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri da gwamnatin shugaba Bola Tinubu, kada su yi zanga-zangar adawa da gwamnati.
