Kotu ta yanke wa ƴan Boko Haram 125 hukunci

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Aƙalla mayaƙan Boko Haram 125 tare da masu ɗaukar nauyinsu ne aka yanke wa hukunci a bainar jama’a a wani zama na kwana biyu a Kainji da ke jihar Nija.

An same su ne laifukan ta’addancin kan iyaka, tallafa wa ta’addanci da wasu lafukan kotun fashin ƙasa-da-ƙasa.

Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, shi ne wanda ke sanya ido kan lamarin hukuncin tare da haɗin gwiwar ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

An gudanar da hukuncin ne a ranakun Talata da Laraba wanda masu shari’a biyar daga babbar kotun tarayya ƙarƙashin jagorancin Binta Nyako su ka gabatar.

Sauran Alƙalan sun haɗa da; Joyce Abdulmalik, Emeka Nwite, Oboira Egwuatu da Mobolaji Olajuwon.

By Babaji