Zanga-zangar tsadar rayuwa: Rundunar ‘Yan sanda ta baza jami’ai 4,200 a Abuja

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Rundunar ‘Yan sandan Abuja ta ɗauki matakin baza jami’ainta a lunguna da saƙo-saƙo na babban birnin sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da wasu masu ƙishin al’umma da matasa su ka shirya yi a faɗin Nijeriya.

Mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Edeh ta bayyana hakan wa manema labarai a ranar Juma’a, inda ta ce sun ɗauki matakin bada kariya wa al’umma ta hanyar yin bincike ga masu zanga-zangar a wurare daban-daban da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro.

Ta ce, Kwamishinan babban birnin, Benneth Igweh a lokacin da ya ke magana akan damar ƴanci da dokar ƙasa ta bai wa al’umma, ya shawarci jama’a da su bada haɗin kai wajen gani an yi zanga-zangar cikin lumana.

Ya kuma yi alkawarin dakatar da tarzoma da ƙin kiyaye doka, yana mai cewa al’umma su zama masu kula gami sanar da jami’ai a duk lokacin da su ka ga wani abin zargi ta lambobi kamar haka; 08032003913, 08028940883, 08061581938, 07057337653 PCB: 09022222352, CRU: 08107314192

By Babaji