Ambaliyar ruwa ta raba mutane 1,700 da matsuguninsu a Sakkwato

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sanata mai wakiltar mazaɓar Sakkwato ta Arewa a Majalisar Dattawa Sanata Aliyu Magatakardan Wamakko ya jajanta wa al’ummar Ƙaramar Hukumar Gada bisa ibtila’in ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje da gonaki da dama.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da mataimaki na musamman ga Sanatan kan harkokin yaɗa labarai, Kwamared Bashar Abubakar ya raba wa manema labarai a Sakkwato ranar Litinin.

Sanata Wamakko wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin tausayi, ya kuma roki Allah Maɗaukakin Sarki da ya kare waɗanda abin ya shafa daga abin da zai faru nan gaba, ya kuma saka musu da mafi alheri.

A cewar sanarwar, sama da mutane 1,700 ne suka rasa matsuguni yayin da gidajensu suka lalace, sannan aka ce kusan kadada 600 na gonaki sun nutse a lokacin ambaliyar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, kauyukan da lamarin ya shafa sun haɗa da; Dantudu, Balakozo, Gidan-Tudu, and Tsitse da dai sauran su.

Ko da yake ba a yi asarar rayuka ba, an kuma yi asarar dabbobi da kayan abinci da dama a yayin lamarin.

By ukarofi