Arewa na kan siraɗi, inji Gwamnan Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana damuwarsa kan yadda ƙananan yara da ba sa zuwa makaranta, talauci da sauran matsalolin tattalin arziki da ake fama da su a Arewa, ya bayyana cewa yankin na daf da wargajewa idan shugabanni ba su haɗu don nemo hanyoyin magance ƙalubalen ba.

Uba Sani ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar ban girma da shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), Mamman Osuman ya kai jihar Kaduna.

Ya ce, “Wannan sabon kwamitin zartarwa ya fito ne a lokacin da ake fuskantar ƙalubale. Muna fuskantar ƙalubalen a ɓangaren cigaba da tsaro. Masu aikata laifuka sun yi wa yankunan Arewa ƙawanya tare da daƙile ci gaban da muka samu ta fuskoki da dama. Rashin ci gaban mu yana da ban tsoro kuma yana buƙatar kulawa da gaggawa.

“A shekarar 2022, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta hannun Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta ƙaddamar da mafi girman ma’auninta na talauci. Binciken ya nuna cewa kashi 63 cikin 100 na mutanen da ke zaune a Nijeriya (wato kusan mutane miliyan 133) talakawa ne masu ɗimbin yawa. Kashi 65% na talakawa (wato mutane miliyan 86) suna zaune a Arewa, yayin da kashi 35% (kusan miliyan 47) ke zaune a Kudu.

“Arewa ba ta da kyau a fannin Ilimi. Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya ce adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya ya kai miliyan 18.3. A cikin wannan mummunan adadin yaran da ba sa zuwa makaranta, kusan kashi 70% na Arewacin Nijeriya ne. Wannan abu ne mai matuƙar tayar da hankali kuma dole ne mu damu a matsayinmu na masu kula da Arewa da Nijeriya gaba ɗaya.

“Kamar yadda na ambata, rashin tsaro a Arewa na ci gaba da ƙaruwa a sassa masu muhimmanci. manoma da yawa ba sa iya shiga gonakinsu. Rashin abinci yanzu yana fuskantarmu kai tsaye. Yawan mace-macen yara da mata na ƙaruwa. Kayan aikin mu sun lalace. Yunƙurin magance giɓin ababen more rayuwa na fuskantar barazanar rashin tsaro.

“Ga Arewa al’umma kuma, ku tashi tsaye don sauya akalar waɗannan matsaloli. Abin takaici, abin da muke gani a Arewa shi ne tallata siyasa mai guba, adawa, da kuma tsarin “danne shi a ƙasa.”

“Mu na shiga cikin zarge-zarge, ba tare da yunƙurin neman mafita ba. Mun kasa yi wa kanmu wasu muhimman tambayoyi. Daga ina ruwa ya fara dukan Arewa? Su wane ne masu hannu a cikin rashin cigaban Arewa?

“Me mu ka yi a ɗaiɗaiku da ƙungiya don nemo hanyoyin magance ƙalubalen da Arewa ke fuskanta? Dole ne mu kalli kanmu da kyau, mu gaya wa kanmu wasu gaskiya kuma mu haɗu tare don tsara dabarun gama gari don magance ƙalubalen ci gabanmu, mu fuskanci masu aikata laifuka da ke sa rayuwa ta zama mai wahala ga mutanenmu.

“Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa na da babban rawar da za ta taka wajen samar da wannan yarjejeniya da ake buƙata domin ingantacciyar hanyar tunkarar ƙalubale iri-iri da ke fuskantar Arewacin Nijeriya. ACF dole ne ta yi ƙoƙari don mayar da hankalin jama’armu. Mu rage martaba siyasa, mu mai da hankali kan ci gaba. Mu himmatu wajen shawo kan barazanar da dukkan ƙarfin da za mu iya samu”.

By ukarofi