Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kasuwar hannayen jari ta Nijeriya ta rufe mako cikin ƙarfi, inda ta ci gaba da tafiyar da take yi ta haɓaka, sakamakon ƙaruwar darajar manyan kamfanoni masu nauyi da suka ja ragamar kasuwanci a ƙarshen mako.
Alƙaluman kasuwar, musamman ma NGɗ All Share Indeɗ (ASI), sun nuna gagarumin ci gaba da kaso 6.57 cikin ɗari a cikin mako guda, inda ya tashi zuwa maki 217,167.57 daga maki 203,770.43 da aka samu a makon da ya gabata.
Wannan ci gaba ya nuna yadda kasuwar ke samun ƙarin ƙarfi tare da jawo hankalin masu zuba jari.
Haka kuma, jimillar darajar kasuwar hannayen jari (market capitalisation) ta ƙaru da kaso 6.60 cikin ɗari, inda ta kai naira tiriliyan 139.83. Wannan ya biyo bayan ƙarin shigar sabbin hannayen jari biliyan 3.62, wanda ya haifar da ribar kusan naira tiriliyan 8.66 cikin mako guda – abin da ya zarce nisan da aka samu a makon baya da ya tsaya a tiriliyan 1.36 kacal.
Wannan ci gaba ya ƙara ɗaga ribar da aka samu tun farkon shekara (year-to-date return) zuwa kaso 39.53 cikin ɗari, alamar cewa kasuwar na ci gaba da tafiya cikin nasara mai ɗorewa.
A ɓangaren yawan kamfanonin da suka samu riba da waɗanda suka yi asara, an samu kamfanoni 61 da darajarsu ta ƙaru, yayin da 36 suka yi faduwa, abin da ke nuna faɗaɗar sha’awar masu zuba jari a kasuwar baki ɗaya.
Harkokin ciniki a kasuwar sun nuna ƙarfi matuƙa, inda yawan mu’amaloli ya aaru da kaso 10.94 cikin ɗari, adadin hannayen jari da aka sayar ya ƙaru da kaso 6.75, yayin da jimillar kuɗin da aka yi mu’amala da su ta haɓaka da kaso 28.53 cikin ɗari idan aka kwatanta da makon da ya gabata.
A jimlace, an yi cinikin hannayen jari biliyan 3.588 da darajarsu ta kai naira biliyan 195.313 cikin mu’amaloli 254,553. Wannan ya nuna yadda masu zuba jari ke ƙara shiga kasuwar fiye da yadda aka gani a baya.
Fannin harkokin kuɗi (financial services) ne ya fi jan ragama a yawan ciniki, inda aka sayar da hannayen jari biliyan 2.498 da darajarsu ta kai naira biliyan 94.005. Wannan ya kai kusan kaso 69.62 na yawan ciniki da kuma kaso 48.13 na jimillar kuɗin da aka yi mu’amala da su.
Sai kuma fannin sabis da ya biyo baya, yayin da fannin mai da iskar gas ya zo na uku, inda shi ma ya taka rawar gani a kasuwar.
Manyan kamfanoni uku—Sterling Financial Holdings Company Plc, Access Holdings Plc da Zenith Bank Plc—su ne suka fi tasiri a kasuwar, inda suka haɗa kusan kaso 28.92 na yawan hannayen jari da aka sayar da kuma kaso 23.59 na darajar mu’amaloli gaba ɗaya.
A ɓangaren sassa, fannin inshora ya ɗan samu koma baya da kaso 0.04 cikin ɗari, sakamakon sayar da hannayen jari a wasu kamfanoni. Sai dai a gefe guda, fannin mai da iskar gas ya jagoranci kasuwar da ƙarin kaso 17.59 cikin ɗari, yayin da fannin bankuna ya biyo baya da kaso 11.85, sannan kayayyakin masarufi suka samu ƙarin kaso 7.76 cikin ɗari.
Masana tattalin arziki na ganin wannan gagarumin ci gaba na nuna yadda kasuwar hannayen jari ta Nijeriya ke dawowa da ƙarfi, tare da ƙara jawo hankalin masu zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje.
