“Ina son a tuna da gudunmawata wajen gyaran aure”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Sunan Hajiya Aishatu Giɗaɗo Idris, wacce aka fi sani Uwa Idris, ba ɓoyayye ba ce a gidaje da dama na arewacin Nijeriya, musamman ma ga masu amfani da zaurukan sada zumunta ko manhajar Facebook, inda take rubuce rubuce na faɗakarwa kan zamantakewa da ba da shawarwari ga ma’aurata. Wannan ƙoƙari da take yi shi ya kai ta ga kafa ƙungiyar sasanta tsakanin ma’aurata da tallafawa matasa ta ‘Initiative for Development of Counseling and Care’, wacce a ƙarƙashin ta aka riƙa ceto rayuwar auratayya da dama da ke gab da rabuwa da kuma faɗakar da matasa muhimmancin gina ingantacciyar rayuwa da barin shaye shaye. Wannan jarumar mata ta shafe tsawon lokaci tana wallafa littattafai cikin harsunan Turanci da Hausa kan ɓangarorin rayuwa daban daban. Wakilin Manhaja , Abba Abubakar Yakubu, ya gana da ita, don jin yadda rayuwarta ta kasance.
MANHAJA: Zan so ki gabatar mana da kan ki.
HAJIYA UWA: An haife ni ne a shekarar 1960 a birnin Zaria da ke Jihar Kaduna. Amma a garin Kaduna na yi makaranta tun daga matakin firamare zuwa sakandire. Amma daga nan ban ƙara zurfafa karatuna ba, daga sakandire na tsaya. Ko da yake na ɗan fara karatun aikin lauya, amma na bari a shekarar farko kuma tun daga nan ban ci gaba ba. Na zauna Sakkwato, a nan na yi auren farko ina da shekaru ashirin a duniya.
Mai ya ja hankalinki kika fara rubuce rubuce na faɗakar da ma’aurata ta shafinki na Facebook?
Abin da ya jawo hankalina shine, son in bayyana labarin zuciyata kuma in ji na wasu, don yin nazari a kai. Da yake ni a rayuwata sha’anin zamantakewa na bani wahala. Ba don komai ba, sai don Allah a nan Ya sha yi min jarrabawa. A dalilin haka ne na yi shawara da zuciyata kan in ƙara bincika abin da ya sa ake yawan samun matsala a tsakanin maza da mata? Sai na fara rubuta na wa, daga nan kuma ra’ayoyin mutane suka ƙara faɗaɗa na wa tunanin har dai na kai inda na kai a yanzu.
Bugu da ƙari abin da ya ƙara jan hankalina kan maganar zamantakewa shine, yadda in ka lura da yanayin magidanta sai ka ga mutun namiji ko mace suna harkokin su kamar da gaske, amma da ka kusance su sai ka ga wauta da rashin sanin makamar ludayin zaman auren su na neman ya lalata gidan auren su. Wato abin nufi a nan shine, ba su san ɗa’ar zaman aure ko sahihancin ɗaukar zamantakewar aure da muhimmanci ba.
A wajen wasu kuma aure al’ada ce kawai. Akwai abubuwa da yawa da nake ganin al’umma na qin ganewa game da zamantakewa, musamman dangane da abin da ya shafi ɗa’a, gyaran lamiri, tsare haƙƙoƙin juna da tsaron gaskiya. A dalilin haka ne nake ba da tawa gudunmawar don kyautata zamantakewar ma’aurata.
Yaya kike kallon tasirin ayyukan da kike yi a rayuwar masu bibiyar rubutun da kike yi?
Alhamdulillah, a gaskiya ina ganin tasirin waɗannan rubuce rubuce musamman ga masu bibiyar rubutun da nake yi. Ina yawan samun saƙonni ta akwatin ajiye saƙonni na wato ‘inbox’, inda wasu ke turo da tambayoyi ko neman shawara, ni kuma ina ba su amsa daidai gwargwado. Wasu ma da suka sanni sosai har gida suke biyoni, don neman a ba su shawara. Da dama sun yarda cewa ina da wata masaniya ko ilimin ba su shawarar da za ta taimake su, su ceci rayuwar aurensu.
Mene ne ra’ayinki game da ƙorafe ƙorafe da ke yawa na cin zarafin juna a tsakanin ma’aurata?
Wato inda matsalar take a ganina shine, kowanne daga cikin jinsin nan biyu sun kasa jurewa su yi haƙuri da yadda rayuwa ta zo musu. Maza na saurin jin haushin mata, su kuma mata na saurin gajiya da haƙuri da halin maza, saboda suna ɗaukar kansu ya waye. To, kuma wayewar kai ba ta taɓa zama rashin tsoron Allah ba. Mu mata mu ne al’umma, saboda haka ya kamata ba yara kaɗai ba har mazan ma mu ba su tarbiyya. Amma ba muje muna kuka da su a ko da yaushe ba.
Kamar yadda yawancin mata ba sa so a faɗa, matan ma suna cin zarafin maza sosai illa dai ba a cika son magana a kai ba ne, don mazan na ƙyalewa kuma matan basa yarda a san suna yi. Sai dai su matan sun fi kai ƙara da faɗin cewan su ake ci wa zarafi. Mata suna kai duka, suna kwaɗa wa miji kofi ko tangaran a kai. Amma idan sun ƙaryata ana yarda. Maza kuma suna zagi, duka da wulaƙanci, kuma ana yarda sun yi, ba musu.
Wacce gudunmawa ƙungiyar ki ta bai wa mata da matasa wajen fahimtar rayuwa da zamantakewa?
Muna da tsare tsare da muka yi na taimakawa, kamar yadda ayyukan ƙungiyoyin sa kai suke, sai dai matsalar rashin samun tallafi da kuɗaɗen gudanarwa suna kashe mana gwiwa. Akwai ayyuka da muka gudanar a baya da suka haɗa da tarukan bita da ƙara wa juna sani, har da muhawara. Ina iya tuna wa mun taɓa shirya wata muhawara a Kano kamar shekaru biyar da suka gabata, inda muka tattauna kan batun wa ke da laifi, namiji ko mace?
Sannan mun bayar da gudunmawa wajen samar da ayyukan yi da sana’o’in dogaro da kai ga matasa da suka daina shaye shaye. A irin ayyukan da muke yi ne har wa yau na rubuta wani littafi mai suna ‘Kace Na Ce’ don sasanta maza da mata da fahimtar da su yadda za su gane bambance bambancen da ke tsakanin juna, saboda a rage yawan zarge zarge.
Wanne ƙalubale mata a yau suke fuskanta wajen fahimtar abokan rayuwar su maza da yadda ya dace su tafiyar da mu’amalar su?
Ƙalubalen da mata ke fuskanta daga abokan zaman su maza sun haɗa da rashin samu lokacinsu. Zamani ya sa maza ba su da lokacin nuna cikakkiyar kulawa ga mata. Mata kuma suna gajiya da kawunan su, sai su shiga wata sabgar da bata kamata ba, har suyi ta sauraron shawarwarin banza. Sannan kuma, maza sun rikiɗe ba su da tabbas ba kamar da ba. Yawanci ba su da alƙawari, kuma ba su damu ko girman su zai faɗi ba. Yayin da mata ke yawan ƙorafin maza ba sa ba su haƙƙin su na abin kashewa da na cefane.
To, ni shawarar da zan bai wa su matan shine, su riƙa neman abin da za su yi (na alheri) domin cika wa kansu lokaci, kafin mazajensu su juyo ta wajen su. Sannan kada su dage da cewan farin cikinsu ya danganta ne kaɗai ga samun hankalin namiji a ko da yaushe. A rikice mazan yanzu suke. Rayuwa tayi wuya. Su tausaya masu suma, domin wata ƙyaliyar da suke yi ba da gangan ba ne. Su rinƙa yi wa mazan su addu’a.
Sannan kada mace ta ce sai ta nuna wa namiji wayo ko ganin iyakarsa, don ta ga yana son ta. Maza ba sa son yawan ƙorafi ko rainin wayo. Kuma ya kamata mu gane cewa ba a sayen namiji da kuɗi, idan kika taimaka masa da bashi ko kyauta ban da gori, ko da tunanin sai kin mallake shi.
Yaya ayyukan da kike yi ke shafar zamantakewar naki iyalin?
Alhamdulillah, a gaskiya ina samun goyon bayan mijina a duk ƙoƙarin da nake yi. Kuma su ma ‘ya’yana suna jin daɗin rubuce rubucen da nake yi, su ma kuma suna ɗaukar darussan rayuwa daga abubuwan da nake rubutawa. Kuma na gode wa Allah da rubutuna ba ya hana ni aiwatar da abin da ya kamata in aiwatar a gidan mijina.
Da wanne abu kike so a riƙa tuna wa da ke?
Ina son a riƙa tunawa da ni a duk lokacin da mutum ya ga abin da ya caza masa ƙwaƙwalwa a kan zamantakewar aure, ya tuna da ni. A tuna da jajircewa ta kan samar da kyakkyawar zamantakewa a tsakanin ma’aurata. Ina fatan a tuna da cewa komai sai an bi shi a ilimince ake samun nasara.
Madalla. Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.