Matakan ƙasar Sin na daƙile COVID-19 sun tabbatar da gudanar wasannin Olympics ba lokacin hunturu na Beijing cikin aminci

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya bayyana a yau Juma’a cewa, ingantattun matakan kandagarki da dakile yaduwar COVID-19 da ƙasar Sin ta dauka, sun tabbatar da karbar baƙunci da gudanar wasannin Olympics na lokacin hunturu da irinsa na nakasassu na 2022, da aka yi a Beijing, cikin aminci ba tare da wata tangarɗa ba.

Xi Jinping ya bayyana hakan ne yau, yayin wani taro don girmama waɗanda suka bada muhimmiyar gudunmawa ga gudanar wasannin 2 na Olympics na Beijing na lokacin hunturu na 2022 cikin nasara.

A cewar shugaban, duk da mummunan tasirin COVID-19 da ake fuskanta a duniya, ƙasar Sin ta sanya kiwon lafiyar dukkan mahalarta gaba da komai, ta kuma ɗauki manufofin kare ƙwayar cutar daga sake shiga ƙasar domin kare sake ɓarkewarta, da kuma tsaurara aiwatar da matakan kandagarki da daƙile ta.

Ya ƙara da cewa, yayin da wasannin ke gudana, kaso 0.45 na jami’an dake karɓaɓɓen wurin gudanar da wasannin ne gwaji ya nuna sun kamu da cutar. Kuma dukkansu sun samu ingantacciyar kulawa. Kana babu wani rukunin mutane da ya kamu da cutar, haka kuma ba a samu yaɗuwarta ba, inda aka tabbatar da babu cutar a birane.

Bugu da ƙari, Xi Jinping ya ce, manufofin ƙasar Sin na yaƙi da annobar, sun haifar da da mai ido, inda suka bayar da gudunmawa wajen gabatarwa duniya darussan yaƙi da annobar da kuma karɓar bakuncin muhimman tarukan ƙasa da ƙasa.

Shugaba Xi Jinping ya ce, kamar yadda ’yan wasannin ƙasashen waje suka bayyana, idan akwai wata ƙasa da ta dace da samun lambar yabo ta fuskar yaƙi da annobar COVID-19, to ƙasar Sin ta cancanta.

Mai Fassara: Fa’iza Mustapha