Tare da CHIROMA AMINU ASID
Wannan ƙwarya-ƙwaryar asibiti ne a tafin hannun ka da mai olsa, wato ‘ulcer’ (ko gyambon ciki), na iya azumin watan Ramadan idan ya yi takatsantsan kuma ya bi wasu shawarwari kamar haka:
1. Tuntuɓi likita kafin Ramadan:
Idan cutar ta yi tsanani, likita zai iya ba da shawarar ko za ka iya yin azumi ko a’a. Wasu magunguna na ‘ulcer’ suna buƙatar a sha su sau da yawa a rana, don haka likita zai iya canza su zuwa masu tasiri na dogon lokaci.
2. Cin abincin da ya dace a sahur da buɗe baki:
Ka rage cin ‘acidic foods’, kamar lemo, tumatir da abubuwan da ke da yaji, ko abu mai zafi ko mai maiƙo sosai. Ka fi mai da hankali kan abinci mai yalwa da ‘fiber’, kamar dawa, gero, shinkafa. Ka sha madara, saboda tana rage ‘acid’ a ciki. Guji shan abubuwa masu gas, kamar lemon kwalba da kuma abinci mai nauyi da maiƙo da yawa.
3. Kada ka yi sahur da wuri:
Yin sahur kusa da safiya na rage lokacin da ciki zai kasance babu abinci. Kamar yadda Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallama ya karantar.
4. Guji Abubuwan da ke ƙara matsalar olsa:
Kada ka sha shayi ko ‘coffee’ mai ƙarfi da zarar ka buɗe baki, saboda suna ƙara ‘acid’ a ciki. Kada ka ci abinci mai nauyi a lokaci ɗaya, sai ka raba kaɗan-kaɗan. Kada ka kwanta da wuri bayan cin abinci, saboda hakan na iya haifar da ‘acid refluɗ’, wanda ke saka olsa ya ta’azzara. Ka guji shan sigari da barasa, idan kana amfani da su, domin suna ƙara tsananin ‘loss’.
5. Amfani da magunguna masu kyau don olsa:
Ka tuntuɓi likita, domin ya rubuta maka magungunan olsa da suka dace da kai.
6. Guji damuwa da gajiya:
Damuwa na iya ƙara yawan ‘acid’ a ciki, don haka yana da kyau a guji damuwa da kuma samun isasshen hutawa. Yin addu’a da karanta Alƙur’ani na taimakawa wajen samun nutsuwa.
Shawara mai muhimmanci ga mai olsa:
Idan ‘ulcer’ ɗinka yana da tsanani har yana haddasa zafin ciki mai tsanani, amai da jini, ko zawo mai jini, yana da kyau ka bar azumi har sai ka warke, ko kuma ka yi amfani da rukhsar da addini ya bayar na ba da fidya idan ba za ka iya yin azumi ba. Idan matsalar ‘ulcer’ ɗinka ba ta da tsanani kuma ka na jin lafiya, za ka iya yin azumi, amma ka bi waɗannan shawarwari, don gujewa matsala.
Allah Ya sa mu dace.
