
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar tsohuwar ƴar jarida kuma matar marigayi MKO Abiola, Dakta Doyin Abiola ta rasu bayan shafe shekaru 82 a duniya.
Wasu daga cikin iyalanta sun tabbatar da cewa marigayar, wadda tsohuwar Darakta Manaja ce a babbar jaridar ƙasa ‘National Concord’, ta rasu ne da misalin ƙarfe 9:15 na dare a ranar Talata bayan fama da wani rashin lafiya na tsawon lokaci.
Dakta Doyin ta kafa tarihi na zama edita mace ta farko a tarihin aikin jarida a Nijeriya wadda ta bada gagarumar gudunmuwa a fannin.
Ta yi karatun digirinta na farko a tsangayar Turanci da wasan kwaikwayo a Jami’ar Ibadan a shekarar 1969, inda daga bisani a 1970 ta tafi Amurka domin yin digiri na biyu a fannin aikin jarida.
A shekarar 1981 marigayi MKO Abiola ya aure ta inda ta yi ta ba shi gudunmuwa a harkar siyasarsa musamman a lokacin da aka soke zaɓensa na ‘June 12’ a shekarar 1993.
Za a cigaba da tunawa da ita musamman kan yadda ta nuna jajircewa a fannin aikin jarida, jagoranci na gari da ma harkokin ƙasa.
