Wani lokaci idan na kalli fim ina samun jigo a cikinsa – S. Reza

Spread the love

“In dai da kayan ƙwalama a kusa na fi jin daɗin rubutu”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

A wannan makon shafin Adabi ya yi gamo ne da wani matashin marubuci daga Jihar Binuwai, wanda ya daɗe yana ba da gudunmawa a harkar rubutun adabi, musamman a shafukan sada zumunta. Salis Reza ba ɓoyayye ba ne a tsakanin marubutan onlayin. Kodayake bai taɓa wallafa littafi ba, amma ya fitar da littattafai kimanin goma a onlayin. A zantawarsa da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, S. Reza ya bayyana masa yadda aka yi sunan Reza ya bi shi. 

MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanka? 

S. REZA: Sunana Muhammad Salisu Adam, amma an fi kirana da S. Reza. Ni marubuci ne, kuma ɗan kasuwa. Ina harkokin kasuwanci daban-daban, don na rufawa kaina asiri. Sannan ni mutum ne mai sha’awar ƙwallon ƙafa sosai. 

Ba mu cikakken tarihin rayuwarka?

Ni dai an haife ni ne a garin Makurɗi ta Jihar Binuwai, amma na girma a Birnin Kudu da ke Jihar Jigawa, kasancewar mahaifina ɗan can ne. Na yi karatuna na firamare a Makurɗi, amma kuma a Jigawa na yi sakandire. Bayan nan na koma gida Makurɗi inda na cigaba da harkokina na kasuwanci. Alhamdulillah!

Me ya sa ake yi maka laƙabi da Reza? 

Ai daga ji an ce Reza to, kasan ZA a sha yanka ne. Ni ina buga ƙwallon ƙafa sosai, wanda a nan ne na samo sunan Reza. Idan na riƙe kwallo duk wanda ya zo sai ya sha yanka, hakan ya sa ake kira na da S. Reza. Kuma ina sa ran in sha Allahu ina da abinci a ƙwallon ƙafa. Har yau wasa idan babu S. Reza ba ya ƙayatarwa.

Yaushe ka fara rubutu? Kuma mene ne silar fara rubutunka?

Na fara rubutu a shekarar 2018, kuma abin da ya sa na fara rubutu ba wani abu ba ne illa sha’awa. Na kasance mutum ne mai son karance-karance da rubutu. Lokacin da na dawo gida da zama daga Jigawa, sai na dawo da yawan rubuce-rubuce da Hausa, wanda kuma a wurin mu zan iya kiransa da sabon abu. Saboda a nan Hausar ma ba isar mu ta yi ba. Ina ganin kamar dai wannan ne dalilin.

Littattafai nawa ka rubuta, kuma nawa ne ka iya bugawa a ciki? 

Na rubuta littatafai kamar tara zuwa goma, sun haɗa da ‘So Ne’, ‘Uwata Ce Sila’, ‘Addininmu’, ‘Ameera Da Adam’, ‘Tsinuwar Uwa’, ‘Ina Muka Dosa’, ‘A Bar Wa Rai’, ‘Gidan Arna’, ‘Mutum Da Aljan’, da kuma ‘Cakwakiyar Soyayya’. Sai dai ban taɓa buga littafi ko ɗaya ba, amma in sha Allahu ina da burin hakan nan gaba.

Yaya alaƙarka take da sauran marubuta da kuma masu bibiyar rubutunka?

Ina da alaƙa mai kyau tsakanin na da dukkanin wani marubuci ko mai karatu, kuma ina girmama kowa muddin ya girmama kansa. Ni a wurina marubuci ɗan’uwa ne na jini, hakan ya sa a duk lokacin da zan yi alaƙa da mai rubutu nake ba shi darajar sa ta ɗan’uwa. Amma duk wanda na lura da cewar ba su da girma sai na jikinsu to, ina jan jikina da su.

Waɗanne hanyoyi ka ke bi wajen zaɓar jigo idan za ka yi rubutu?

Hanyoyi da yawa. Wani lokaci idan na kalli fim ina samun jigo a cikinsa, wani lokaci ma har littafi idan na karanta. Sannan na kan zauna na yi nazari akan wani abu da ya dame ni, ko yake damun wanda ke kusa da ni, ko dai wanda na taɓa ji ko gani. Na kan zauna na tsara abin da nake ganin zai iya kawo maslaha ko mafita akan wannan abin, sai na yi rubutu a kai. Ko kuma kawai na je wani wuri na ga abin da ya bani mamaki, shi ma ina iya yin rubutu akai.

Idan da za a ba ka damar kawo sauyi a wasu matsaloli da ke ci wa marubuta tuwo a ƙwarya da wacce matsala za ka fara?

Zan iya magance matsalar rashin tsaron da ake samu ga marubuta da kuma wasu daga cikin makaranta ta ɓangaren cinikayyar littafi da kuma yawan ɗaukar wa mutum littafi a fara karantawa ba tare da sanin sa ba. Abin na min ciwo sosai. Ban sani ba, ko don na san zafin abin ne! Na kan shiga irin wannan faɗan a yi da ni, wanda ta dalilin haka an sha a kawo min ƙorafi akan masu irin wannan abin. Kuma cikin yardar Allah da yake ina da kusancin da wasu daga cikin makaranta na manhajar YouTube sai ka ga an samu maslaha. To, gaskiya a taƙaice dai wannan zan fara magancewa ta yadda duk wanda aka samu da irin wannan cin amanar to, zai biya tara mai yawa.

Ya ka ke kallon rubutu a jiya da yau ta fuskar cigaba da koma baya?

E, to! An samu cigaba sosai ta wasu ɓangarorin, sannan kuma a wani ɓangaren zan iya cewa an samu rashin cigaba. A da marubutan ba su da yawa, kuma yawanci hanya ɗaya ce suke iya bi domin sayar da littafinsu, idan ka ji yadda wata ma take shan wahala wajen sayar da littafi bayan wahalar rubutu sai ka sha mamaki. Sannan a da babu wata hanya da za a dinga fitar da littafi kamar yadda ake yi yanzu, wanda ana saya a onlayin, sannan bayan ka gama kuma ka sake sayar dashi a dunƙule ta document. Amma a baya har sai ka kammala kafin ka biyu kuɗin bugawa, sannan a kai kasuwa a sayar. Ta nan dai kam an samu cigaba. Ta ɗaya ɓangaren kuma yanzu da aka samu yawaitar marubutan sai kuma ya zama kamar taron tsintsiya ba shara. Domin idan za a ɗauki littafin da ya zama zakaran gwajin dafi na da da kuma na yanzu, sai ka samu bambancin darasi da kuma isar da saƙo fiye da na yanzu.

Me za ka iya cewa game da tasirin marubuta a cikin al’umma?

Kamar yadda kowa ya sani ne marubuci fitila ne mai haske da ke haskawa al’umma hanyar tafiyarsu, marubuci ne mai kallo abu da ido huɗu saɓanin sauran halittu da suke kallo da ido biyu. Shi marubuci kullum ƙoƙarin sa ta yaya zai haskawa mutane wani abu da basa iya ganin sa a cikin duhu. Tsarin marubuci tamkar malami ne a cikin aji.

A wane yanayi ka fi jin daɗin yin rubutu, kuma me ya sa?

Nafi jin daɗin yanayin farinciki, sannan lokacin kaɗaici, a ce babu kowa a kusa da ni. Sannan ina jin daɗin yin rubutu idan akwai ɗan abin motsa baki a kusa da ni, kamar dai nama ko cincin ko kuma abu mai sanyi kamar madara da sauransu. Tabbas za a samu abin da ake so a wannan lokacin.

Duk wani abu na rayuwa tattare yake da ƙalubale da nasarori, ko za mu iya sanin wasu daga cikin nasarori da ƙalubale da suka shafi rubutunka?

Bari na fara da ƙalubale. Gaskiya na samu ƙalubale masu tarin yawa lokacin da na fara rubutu. Kaɗan daga cikin kuwa su ne. Lokacin da na fara rubutu ban san wani marubuci ko marubuciya ko ɗaya ba, sannan inda nake suna kallon abin kamar ƙauyanci da rashin aikin yi. To, kuma dama ni ɗalibi ne. To, sai ake yawan faɗa min wannan abin bashi da amfani, har na kan yi rubutun kuma na karanta kayana kuma na yaga takardar. Daga ƙarshe ma sai idan na yi na ɓoye, kai har ta kai ta kawo ma ina ɓoye kaina sai na nuna cewar na iya. Yayye da ƙannai na kuwa da yake dama kamar yadda na faɗa ba kowa ne ya iya Hausa mai kyau a wurin mu ba, sai ya zama basa ma iya karantawa, sai suce to, na yi na turanci mana. Haka dai na dinga fama da yake rai da zuciya na so, sai na daina saka sunan Salis a ciki kawai sai na yi rubutu ba suna. Har dai Allah ya yi na haɗu da Hafsat Garkuwa, sakamakon karata labarina da wata ta yi a facebook, shi ne ta bani wasu shawarwari, har ta haɗa ni da ita.

Na samu nasarori masu yawa ta hanyar rubutu. Babbar nasarar da na samu ita ce ta sanin mutanen kirki, kuma su ma suka sanni. Alhamdulillah a yanzu na gamsar da masu ganin cewar rubutun da nake yi ba abin banza ba ne, duba da ko su suna son karanta labarina idan na rubuta, kuma bana ba su a kyauta sai kowa ya saya, domin ba abin banza ba ne! 

A cikin jerin marubutan onlayin da masu bugawa waɗanne ne gwanayenka, ko kuma waɗanda ka ke kallo a matsayin allon kwaikwayo ko iyayen gida?

Gaskiya kafin na fara rubutu ban taɓa karanta littafin Hausa ba, sai dai irin wannan ƙananan littattafan nan masu shafi biyar, wasu tatsuniya ko soyayya ko dai Hikaya. Hakan ya sa ban san masu bugawa sosai ba, sai dai a nan kusa zan iya kiran Fa’iziyya D. Sulaiman a matsayin allon kwaikwayona, tunda na karanta littattafanta. Marubutan onlayin kuwa suna da yawa sosai, domin duk wata marubuciya da nake jin daɗin littafinta, kuma nake mata kallon allon kwaikwayo to, ina da kusanci da ita, saboda ƙaruwa da nake yi daga rubutun ta. Amma duk da haka akwai wasu marubuta guda biyu da nake ganin ƙimarsu sosai, wato Hafsat Garkuwa, da Batul Mamman. 

Ka taɓa shiga gasar rubutu ka yi nasara?

E! Na taɓa shiga kuma na yi nasara amma ban ci ba. Ina son shiga gasa amma wasu lokutan rashin lokaci ke sa bana shiga. Na taɓa shiga gasar da ake yi a zauren Marubuta na majalisar WhatsApp sau ɗaya, amma ban ci ba. Sai kuma gasar da Kangala Global Writers ya saka, har ga Allah ba zan taɓa mantawa da ita ba. Domin sai da na gama ƙure basirata, amma mutumin nan ya yi mana haranbau ya ƙi fitar da sakamakon gasar. To, har yanzu dai labari na na hannunsa kuma wallahi ban haƙura ba, domin nasa ran zan ci. To, wannan ne gasar kawai da na taɓa shiga. Sai kuma wata ƙaramar gasar muhawara da ƙungiyata ta First Class ta taɓa sawa a shekarar 2022 na zo na ɗaya. Haƙiƙa ina alfahari da wannan gasar. Amma in sha Allahu zan dage na dinga bai wa gasa muhimmanci sosai, domin na san akwai alfanun hakan ga marubuci.

Shin ka taɓa yin wani rubutu da ka yi danasani a kansa?

E, na yi. Amma cikin ikon Allah har yau ban fitar da labarin ba. Na so na fitar da shi amma Allah ya tsare ni. Gaba ɗaya labarin ban yi bincike mai kyau ba na rubuta, sai da kuma na fara fitar da shafin farko sai na hango kuskuren da ke cikin sa, wanda babu wanda ya faɗa min. Yanzu dai haka ina so na inganta shi sai na fitar in sha Allahu.

Wacce shawara za ka bai wa sababbin marubuta da masu sha’awar fara rubutu?

Shawarata ita ce, don Allah a dinga yin bincike kafin a rubuta abu, musamman matsalar da ta shafi addini da ta al’umma. Sannan mu ƙara haƙuri da ƙoƙarin inganta rubutun mu, wanda ko zuwa gaba ba za mu ji kunya ba. Sannan mutum ya kama mutuncin sa, ban da shiga wurin da ba a ganinka da ƙima, idan ma ya zama dole sai an shiga to, a tsaya daga baya-baya.

Idan da za ka bar garin ku, ina kake so ka zauna a ƙasar nan? Kuma me ya sa?

Ina son zama a Jihar Jigawa, saboda na taɓa zama a can, kuma har abokai ne da ni. Na ji daɗin zama da su, mutanen Jigawa suna da kirki sosai. 

 Me ya fi burge ka a rayuwar marubuta? Kuma me ya fi ba ka haushi?

Abin da ya fi burgeni shi ne yadda alaƙa ta zumunci ke ƙulluwa tsakanin marubuta, ba tare da sun san juna ba. Har ka ga an samu zumunci mai ƙarfi da fahimtar juna, har da taimaka wa juna idan buƙatar hakan ta taso. Ba na jin daɗi in ga marubuci na nuna shi wani ne, yana jiji da kai a tsakanin ýan’uwa marubuta. 

Marubuta da dama suna komawa rubutun fim, ka taɓa rubuta labarin fim ne? 

Gaskiya ban taɓa rubuta labarin fim ba, amma an taɓa gayyata ta, a lokacin kuma bani da lafiya, ban samu damar zuwa an yi da ni ba. Amma yanzu in sha Allahu, a shirye nake idan na samu damar haka.

Ko kana da ra’ayin auren ýar’uwarka marubuciya? 

E, zan iya idan har mun fahimci juna. 

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarka? 

Karin magana da take tasiri a rayuwata ita ce ‘Ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali yin wanka’

By ukarofi