Matasan Kasuwar Wayar Rijiyar Lemo sun nemi tallafin jari daga gwamnatin Kano – Salihu Ahmad

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Shugaban ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Wayar Rijiyar Lemo, Salihu Ahmad, ya buƙaci Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf da ta tallafa wa matasan kasuwar da jarin kasuwanci domin bunƙasa sana’arsu.

Salihu Ahmad ya bayyana cewa kasuwar ta tara matasa masu yawa da suka rungumi sana’ar sayar da waya da gyaranta, amma suna fuskantar ƙalubalen rashin isasshen jari wanda ke hana su faɗaɗa harkokinsu.

A cewarsa, gwamnatin Kano na da kyakkyawan suna wajen tallafa wa matasa da al’umma, don haka suna fatan za a duba buƙatarsu, ko da ta hanyar rancen kuɗi mai sauƙin biya domin ƙarfafa musu guiwa.

Ya ƙara da cewa a halin yanzu akwai matasa sama da 1,000 da ke gudanar da sana’o’i a kasuwar, lamarin da ya taimaka wajen samar da ayyukan yi, ƙara bunƙasar tattalin arziƙi da kuma rage zaman banza da ka iya jefa wasu cikin aikata miyagun laifuka ko shaye-shaye.

Salihu Ahmad ya bayyana cewa kasuwar na taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsaro da zaman lafiya a yankin, domin matasa sun samu abin yi da zai hana su fadawa halaye marasa kyau.

A nasa ɓangaren, Sakataren ƙungiyar, Aminu M. Yusif, ya yaba wa shugabannin kasuwar da ‘yan kasuwa kan haɗin kai da zaman lafiya da suke nunawa. Ya kuma jaddada buƙatar tallafin jari daga gwamnati da masu hannu da shuni domin ƙara faɗaɗa kasuwancin matasan.

Ya kuma yaba wa hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kan irin goyon bayan da suke bai wa kasuwar, yana mai fatan za a ci gaba da samun haɗin kai domin bunƙasa sana’o’in matasa a Kano.

By ukarofi