Matashi ya yi ajalin matar aure a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani matashi mai suna Hassan Ɗan Canji ya yi sanadiyyar mutuwar wata Rakiya, wadda iyalin wani Malam Maikuɗi ce da ke Ƙauyen Dambo a Ƙaramar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin, Malam Tukur Dambo ya shaida wa manema a wata hira ta waya cewa al’amarin ya auku ne a daren ranar Alhamis wayewar Juma’a bayan matashin ya yi hatsaniya da matar.

“Bayan hatsaniyar, sai ya shiga gida ya ɗauko adda, sannan ya daɓa mata har lahira”, inji shi.

A cewar mazaunin, ganin haka ke da wuya, ‘yan uwar matar suka mayar da martani ta hanyar lakaɗa masa duka har lahira.

Daga lokacin ne ‘yan sanda suka hallara a wajen da al’amarin ya faru, inda cikin hanzari suka garzaya da gawarwakin biyu zuwa babban asibitin Bakura.

Saidai yunƙurin ji ta bakin Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar ya ci tura kasancewar wakilinmu bai same shi ta waya ba.

By Babaji