
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar APC a Jihar Ribas, ta yaba wa matakin fadar shugaban ƙasa na jaddada Gwamna Siminalayi Fubara a matsayin jagoran jam’iyyar a jihar, tana mai cewa hakan ya fito da ainihin matsayar jam’iyyar a jihar.
APC ta kuma nuna godiya matuƙa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa tsayuwa tsayin daka akan dokokin jam’iyyar wajen jaddada matsayin gwamnan ta mai taimaka masa akan tsare-tsaren sadawa, Danie Bwala.
A sanarwar da APC a Jihar ta fitarta hannun Kakakinta, Darlington Nwauju a ranar Juma’a, jam’iyyar ta ce hakan da fadar ta yi ya nuna haƙiƙanin matsayar APC akan al’amarin, sannan ya yi daidai da salon kiyaye dokokin jam’iyyar na Shugabanta na ƙasa Nentawe Yiltwatda da Sakatarenta na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru.
A cewarta, jaddada matsayin Fubara na jagorancin APC a Ribas ya kore dukkan wani ruɗani ko ƙarairayi da ‘yan kanzagin siyasa ke yaɗawa.
Kazalika, APC ta yi watsa da ra’ayin da Mista Felix Morka ya gabatar na neman tsige gwamnan da mataimakiyarsa, lamarin da ya saɓa wa ƙa’idar zama mamba a jam’iyyar.
