
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya sake jaddada cewa ba zai taɓa sayar da kyawawan manufofinsa na siyasa ba domin riba ta ƙashin kansa.
Kwankwaso ya bayyana haka ne sa’o’i da yaronsa na siyasa kuma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ciyamomi da ‘yan majalisar dokokin jihar da ta tarayya suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar.
Tsohon gwamnan na Kano ya faɗi haka ne a yayin jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Kano, inda ya ce tsawon lokaci da ya ɗauka a fagen siyasa ya samu ne don inganta rayukan talakawa da kare muradunsu.
“Ni ba na sayerwa ba ne. Aƙidun siyasata ne ke tsare ni. Da don riba ba ce, da tuni na bi wata hanya mai sauƙi, ba za ku same ni a nan ba”, inji Kwankwaso.
Ya ce, tafiyar Kwankwasiyya ta samo asali ne daga aƙida da hangen nesa na bai ɗaya, ba daga al’amuran kuɗi ba.
Kwankwaso ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su fara shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 tun daga yanzu, yana mai gargaɗin kada a yi sakaci da halin da ake ciki na buƙatar siyasa mai tsafta.
A ƙarshe, Kwankwaso ya tabbatar wa magoya bayan nasa cewa zai cigaba da tsayawa tsayin daka kan muradun talakawa domin ganin an inganta musu kowane fanni na buƙatar rayuwar yau da kullum.
