Gwamna Raɗɗa ya halarci buɗe masallacin Juma’a mai cibiyar islamiyya da koyon sana’o’i a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗaruruwan al’ummar Musulmi suka halarci bikin buɗe sabuwar masallacin Juma’a tare da makarantun islamiyya masu koyar da sana’o’i, wadda Gidauniyar Sautus Sunnah Charity Foundation ta gina a Kadarko Estate, Katsina.

Sheikh Abubakar Lawal Triumph ne ya gabatar da hudubar Juma’a, inda ya yi kira ga Musulmi da su tsaya tsayin daka wajen tabbatar da haɗin kai, haƙuri da hidima ga al’umma, bisa koyarwar Musulunci.

Da yake jawabi bayan sallar, Gwamna Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya yabawa Gidauniyar bisa jajircewarta wajen bunƙasa ilimin addini, tarbiyyar ɗabi’a da ci gaban al’umma, inda ya bayyana aikin a matsayin “zuba jari mai daraja ga makomar ruhaniya da ilimi na ‘ya’yanmu da al’umma baki ɗaya.”

“ Na ji daɗin rawar da ƙungiyoyin addini kamar Sautus Sunnah Charity Foundation ke takawa wajen tallafa wa ilimi, jin ƙai da zaman lafiya”inji Dikko.

“Wannan masallaci da makarantun Islamiyya za su zama cibiyoyin ibada, koyo, tarbiyya da gina ɗabi’a,” in ji Gwamnan.

Gwamna Raɗɗa ya kuma yaba wa malamai da jagororin addini da suka halarci taron, tare da jinjinawa shugaban gidauniyar, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, bisa ƙwazonsa wajen da’awah, ilimi da ayyukan jin ƙai a faɗin jihar da Arewa baki ɗaya.

Tun da farko, Babban Sakataren Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) na ƙasa, Sheikh Kabir Gombe, ya jaddada muhimmancin irin waɗannan ayyukan alheri wajen ƙarfafa al’umma, tare da tabbatar da goyon bayan ƙungiyar ga makamantan ayyuka nan gaba.

Sautus Sunnah Charity Foundation ƙungiya ce ta addinin Musulunci mai zaman kanta da ke Nijeriya, wadda ke da ƙarfi a Jihar Katsina, tana mai da hankali kan koyar da Alƙur’ani, karatun addinin Musulunci, koyon sana’o’i da tallafa wa marasa galihu.

Ta hanyar cibiyoyi kamar gidan marayu da cibiyar koyon sana’o’i ta JIBWIS Gidan Mariya da ke Kaita, da Makarantar Sautus Sunnah, Gidauniyar na da niyyar haɓaka zuri’a mai ingantaccen ilimi, imani da sana’o’in dogaro da kai, domin su zama ‘yan al’umma masu amfani da ɗaukar nauyi,”inji Kabir Gombe.

Gidauniyar dai na gudanar da ayyukan da’awah, wa’azuzzuka, shirye-shiryen hardar Alƙur’ani, gasa-gasa, bukukuwan yaye ɗalibai da kuma gina masallatai ga al’ummomin da ke buƙata.

Bikin ya samu halartar mataimakin Gwamna, Alhaji Faruk Lawal; Kakakin Majalisar Dokoki, Rt. Hon. Nasir Yahaya; Wakilin Musawa/Matazu a Majalisar Tarayya, Hon. Abdullahi Aliyu (General); Shugaban majalisar malamai ta na JIBWIBS ta ƙasa, Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo; Babban alƙalin alƙalan jihar Katsina.

By ukarofi