2027: Kwamitin matasa na Nasarawa ta Yamma ya kammala ziyarar neman goyon baya ga Farfesa Kana

Spread the love

Daga JOHN WADA a Keffi

Wani kwamitin matasa na tuntuɓa na Nasarawa ta Yamma da ake kira Nasarawa West Youth Consultative Committee a turance dake yaɗa goyon bayan Farfesa Abdulkarim Abubakar Kana (SAN) wato ɗan takarar kujerar sanatan mazaɓar Keffi ta Yamma a majalisar dattawa ta ƙasa a zaɓen 2027 ya kammala wata ziyarar neman goyon baya na musamman na farko ga mai neman takarar sanatan a ƙaramar hukumar Kokona na jihar da sauran ƙananan hukumomi biyar da ke yankin baki ɗaya.
Ziyarar tuntuɓar an faro ne a ranar Litinin na mako da ya gabatar a ƙaramar hukumar Toto inda mataimakin shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar da goyon bayan karamar hukumar wa ɗan takarar da hakan ya kafa tubalin neman goyon bayan al’ummar yankin Nasarawa ta Yamman baki ɗaya musamman matasa ƙarƙashin jagorancin shugaban tafiyar wato Comr. Ja’afar Muhammad Loko.

Manufar ziyarar shine don tabbar da nasarar Farfesa Kana ta wannan ƙoƙari da kwamitin ke yi a yankunan karkarar don kwamitin ta tabbata ɗan takarar wanda sanannen babban lauya masanin harkokin shari’a a jihar da ma ƙasa baki ɗaya zai gudanar da shugabanci nagari da zarar yayi nasarar lashe zaɓen a shekara mai zuwa na 2027.

A yanzu haka wakilin mu a jihar John Wada ya kuma ruwaito cewa kwamitin ta kammala ziyarar tuntuɓar na musamman a duka ƙananan hukumomin shiyar Nasarawa ta Yamman tare da murnar kammalawar cikin Lafiya.
Ƙananan hukumomin shiyar ta Nasarawa ta Yamman da kwamitin ta zagaya sun haɗa da ƙaramar hukumar Toto da Karu da Kokona da Keffi da Kuma Nasarawa inda tuka al’ummar da kwamitin ta tuntuɓe su a yayin ziyarar da suka haɗa da masu zuwa da tsaki da shugabanni a duka matakai da matasa da mata da sauran su duk sun yi alƙawarin haɗa kai da kwamitin don tabbatar da nasarar Farfesa Abdulkarim Abubakar Kana a zaɓe mai zuwa 2027 na sanatan yankin Nasarawa ta Yamma.

By ukarofi