Matashi ya yi barazanar ƙin biyan bashin PalmPay bayan yi masa fallasa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani matashi ɗan Nijeriya ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan ya zargi kamfanin PalmPay da yi masa tsangwama dangane da biyan bashin da ya karɓa. A cikin wani bidiyo da ya bazu a yanar gizo, matashin ya bayyana cewa duk da cewa kamfanin OPay na binsa bashin naira 800,000, abin da suke yi kawai shi ne kiran tunatarwa cikin ladabi, saɓanin PalmPay da ya ce sun fara tuntuɓar mutanen da ke cikin jerin lambobinsa bayan kwanaki kaɗan da bashin ya ƙare.

Ya nuna takaicinsa kan abin da ya kira salon karɓar bashi mai tsauri, inda ya gargaɗi kamfanin da ya daina tuntuɓar mutanen da ke cikin wayarsa. Matashin ya kuma yi barazanar cewa idan aka ci gaba da irin wannan hali, zai iya dakatar da biyan bashin gaba ɗaya tare da daina amfani da manhajar.

A cikin kalamansa, ya zargi wasu ma’aikatan kamfanin da nuna rashin haƙuri, yana mai cewa ba shi da abin kunya da zai hana shi fallasa irin wannan lamari, tare da gargaɗin cewa duk wani saƙo da aka sake turawa wani daga cikin lambobinsa na iya sa ya janye gaba ɗaya daga biyan bashin.

Bidiyon ya jawo martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu ke goyon bayan kamfanin wajen bin diddigin bashin, yayin da wasu kuma ke ganin salon karɓar bashin ya wuce gona da iri.

Wasu masu sharhi sun tunatar da shi cewa jinkirta biyan bashi na iya haifar da ƙarin kuɗi da ke taruwa a kullum, yayin da wasu suka soki halayen karɓar bashi ba tare da shirin biya ba.

Haka kuma, wasu sun yi gargaɗi kan illar rashin kyakkyawan tarihin bashi, suna mai cewa bayanan cibiyoyin tantance bashi na iya ci gaba da kasancewa tare da mutum, kuma su shafi shi a nan gaba.

Sai dai wasu sun nuna tausayi ga matashin, suna mai cewa lamarin ya nuna irin matsin tattalin arziki da wasu ’yan Nijeriya ke fuskanta a yau.

By ukarofi