Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC), ya sanar da ƙulla yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da wasu kamfanonin ƙasar Chana guda biyu domin binciko yiwuwar haɗin gwiwa wajen kammala gyare-gyare da kuma gudanar da ayyukan matatun man fetur na Fatakwal da Warri.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar 3 ga Mayu, 2026, wadda Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na kamfanin, Andy Odeh, ya sanya wa hannu.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Jiaɗing na ƙasar Chana a ranar 30 ga Afrilu, 2026, inda Babban Daraktan Rukunin Kamfanin NNPC, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya sanya hannu tare da Shugaban Kamfanin Sanjiang Chemical, Guan Jianzhong, da kuma Shugaban Kamfanin ɗinganchen (Fuzhou) Industrial Park Operation and Management Co. Ltd, Bill Bi.
A ƙarƙashin wannan shiri, kamfanonin na Chana za su taimaka wajen kammala sauran ayyukan gyaran matatun guda biyu, tare da shiga cikin gudanarwa da kula da su domin tabbatar da ingantaccen aiki mai ɗorewa.
Haka kuma, haɗin gwiwar zai duba yiwuwar faɗaɗa da sabunta matatun domin su dace da sabbin ƙa’idojin man fetur mai tsafta, inganta ribar aiki, da kuma ƙara ƙarfin samar da sinadarai na petrochemical. Ana kuma sa ran shirin zai taimaka wajen bunƙasa cibiyoyin masana’antu da ke dogaro da iskar gas a kusa da matatun.
Yayin da yake jawabi bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, Ojulari ya bayyana hakan a matsayin babban ci gaba bayan watanni na tattaunawa tsakanin ɓangarorin.
Ya ce: “Dukkan ɓangarorin sun fahimci damar da ke akwai ta amfanar juna wajen bunƙasa kadarorin tace mai na NNPC tare da tabbatar da ɗorewarsu a nan gaba.”
Ya ƙara da cewa, yarjejeniyar na daga cikin manyan matakan da ake ɗauka domin samun abokan hulɗa na fasaha wajen gyara da faɗaɗa matatun ƙasar, tare da buɗe ƙofofi a fannonin petrochemical da masana’antun da ke amfani da gas.
Sai dai Ojulari ya bayyana cewa yarjejeniyar ba ta da cikakken ɗauri a halin yanzu, domin tana buƙatar amincewar hukumomin da suka dace da kuma ci gaba da tattaunawa kafin a kammala.
A shekarar 2021 ne aka amince da aikin gyaran Kamfanin Matatar Man Fetur ta Fatakwal kan kuɗin da aka kiyasta dala biliyan 1.5, inda aka bai wa kamfanin Saipem na ƙasar Italiya da sauran abokan hulɗa kwangila domin dawo da ƙarfin tace ganga 210,000 a kowace rana.
Haka zalika, Kamfanin Matatar Warri da Petrochemical na cikin aikin gyara a ƙarƙashin kwangilar da ta kai kusan dala miliyan 897, domin dawo da ƙarfin tace ganga 125,000 a rana tare da haɗa samar da sinadarai.
Dukkanin waɗannan ayyuka na daga cikin babbar dabarar NNPC na rage dogaro da shigo da kayayyakin man fetur daga ƙasashen waje.
Matatar Fatakwal ta taɓa komawa aiki na ɗan lokaci a ƙarshen shekarar 2024 bayan dogon lokaci ba ta aiki, amma daga bisani aka sake rufe ta sakamakon matsalolin gudanarwa da kuɗi.
