Matashi ya yi barazanar kashe kansa bayan hawa allon talla a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano ta ce ta ceto wani ɗan shekara 19 mai suna Ibrahim Abubakar, wanda ɗan Jihar Adamawa ne bayan hawa saman allon talla dake kusa da gadar Ado Bayero da nufin kashe kansa.

Lamarin ya auku ne a ranar 23 ga watan Yuni, 2025.

Matashin ya yi ikirarin faɗowa daga saman allon matuƙar bai ga ɗan TikTok Abdul BK ba.

Mataimakin Kakakin ƴan sandan, DSP Hussaini Abdullahi ya ce bayan samun rahoton ne jami’an ƴan sanda suka garzaya wajen da abin ya faru da haɗin-gwiwar tawagar jami’an kashe gobara.

Bayan ceto shi ne aka gaggauta kai shi Asibitin Police na Bompai sakamakon shafe sa’o’i ba tare da cin abinci ba.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori ya yaba wa jami’an bisa hoɓɓasa da suka yi wajen dakatar da faruwar al’amarin.

Ya kuma umarci a yi binciken mai zurfi akan al’amarin a ƙoƙarinsu na tabbatar da tsaro ga al’umma.

By Babaji