Najeriya da Brazil sun ƙulla yarjejeniyar haɗin gwiwa a fannin fina-finai da ƙirƙira

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Najeriya da Brazil sun rattaɓa hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya da za ta bai wa ƙasashen biyu damar haɗa kai wajen samar da fina-finai, shirye-shiryen talabijin, fina-finan zane (animation), da sauran ayyukan bidiyo. Wannan yarjejeniya mai suna Audiovisual Co-Production Agreement na nufin bunƙasa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a fannin al’adu da ƙirƙira, tare da ƙara wa ƙasashen haske a matakin duniya.

Wannan yarjejeniya za ta bai wa masu ƙirƙira a Najeriya da Brazil damar cin moriyar tallafi da abubuwan jin daɗi da kowace ƙasa ke bayarwa ga masu masana’antar nishadi.

Kasashen biyu waɗanda su ne mafi yawan baƙaƙen fata a duniya na da tarihin haɗin gwiwa na dogon lokaci, kuma wannan sabon mataki yana da nufin haɗa ƙarfi wajen ba da labarai masu ma’ana daga ɓangarorin biyu.

Ministar harkokin al’adu, yawon buɗe Ido da tattalin arzikin Ƙirƙira ta Najeriya, Hannatu Musa Musawa, ta bayyana yarjejeniyar a matsayin “gadar ƙirƙira ” tsakanin nahiyoyi da al’adu. Ta ce, “Wannan yarjejeniya ba wai kawai yarjejeniyar diflomasiyya ba ce, amma wata hanya ce ta sada duniya da labaran Afirka da Afro-Brazil, da kuma buɗe damar aikin yi ga matasa da masu ƙirƙira.”

An bayyana cewa shirin na daga cikin manyan tsare-tsaren da Najeriya ke aiwatarwa na faɗaɗa masana’antar ƙirƙira ta ƙasa, musamman ƙarƙashin shirin “Nigeria Everywhere” da “Destination 2030.” A makonni masu zuwa, ana sa ran za a fitar da cikakkun tsare-tsaren aiwatar da yarjejeniyar, ciki har da shirye-shiryen musayar ma’aikata da masu ƙirƙira tsakanin ƙasashen biyu.

By ukarofi