Daga USMAN KAROFI a Abuja
Gwamnatin Iran ta musanta cewa ta harba makamai masu linzami a kan Isra’ila bayan ƙaddamar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma ƙarƙashin jagorancin Amurka. Wannan na zuwa ne duk da cewa rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta tabbatar da cewa an harba makamai biyu zuwa arewacin ƙasar da safiyar ranar Talata.
Rahoton kamfanin dillancin labarai na ISNA mai alaƙa da gwamnatin Iran ya bayyana cewa rahotannin da ke cewa an harba makami daga Iran bayan tsagaita wuta “ƙarya ne,” kuma gwamnatin Tehran ta musanta kowane irin hannu da ta ke da shi a harin da aka kai bayan ƙulla yarjejeniyar.
Sai dai IDF ta bayyana cewa makaman guda biyu da aka harba sun sa an kunna ƙararrawar gargaɗi a wasu sassan Arewacin Isra’ila, inda mazauna yankin suka shaida cewa sun ga yadda aka harbo makaman a sama. Rundunar ta ce an yi nasarar daƙile harin ba tare da samun hasarar rayuka ko dukiya ba.
Har yanzu hukumomin Isra’ila ba su maida martani kai tsaye kan musun da Iran ta yi ba, sai dai sun bayyana cewa za su “ɗauki matakin ramawa cikin ƙarfi ” idan aka karya yarjejeniyar tsagaita wutar. Wannan sabon rikici na iya ƙara dagula alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu duk da matakin zaman lafiya da aka ɗauka.
