Matatar Ɗangote ta haɗa kai da MRS don sayar da fetur a N935

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Matatar Ɗangote ta ce ta haɗe kan ne da Kamfanin MRS don fara sayar da litar fetur a N935 a baki ɗaya gidajen mansu na Nijeriya a ƙoƙarinsu na sauƙaƙa wa al’umma.

Hakan na zuwa ne bayan Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL) ya sanar da rage farashin lita zuwa ƙasa da N1,000.

A wani rubutu da aka wallafa a shafin X, Shugaban rukunin Kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa ƙoƙarinsa na amfani da naira a yayin gudanar da kasuwancin ɗanyen mai wanda hakan ya yi sanadiyyar rage farashin fetur a ƙasar.

Sanarwar ta ce tuni raguwar farashin ta fara aiki a Legas inda kuma ake sa ran ta fara aiki a ko’ina a Nijeriya wanda hakan ya sa kamfanin ya haɗa kai da MRS.

Ya ƙara da cewa, matatar Ɗangote an samar da ita ne don amfanin al’ummar Nijeriya, don haka ne suke ƙoƙarin samar da fetur mai inganci da kuma rangwamen farashi.

A watan Satumba ne Majalisar Zartarwa (FEC) ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu ta amince da sayar da ɗanyen mai da fetur ga matatun gida ta hanyar amfani da Naira a madadin kuɗaɗen ƙasashen waje.

By Babaji