
Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayyana ƙudirinsa na hukunta duk waɗanda suka ƙi biyan haraji a shekarar 2025, inda ya bayyana shirin gwamnatinsa na yunkurin samar da kuɗin shigar da bai gaza Naira bilyan 80 a sabuwar shekarar ba.
Ya kuma buƙaci kwamishinoninsa da manyan sakatarorin gwamnati da sauran masu-ruwa-da-tsaki da su ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan da za su kawo ma ci-gaba a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakane a yayin da yake rufe taron Majalisar Zartarwa da manyan sakatarorin gwamnatin Kano na kwanaki uku da aka gudanar a ɗakin taro na 17 Hotel dake jihar Kaduna.
Gwamnan ya ce an gudanar da taron ne don samar da kyakkaywar alaƙa tsakanin kwamishinoni da manyan sakatarorin gwamnati kan yadda za’a gudanar da aiki tare.
Haka zalika gwamnan ya kuma kara da cewa gwamnatinsa a tsaye take wajen biyan dukkan haƙƙoƙi na tsofaffin ma’aikata da suka ajiye aiki don inganta rayukansu.
A wani ɓangaren kuma gwamnan ya yi tsokaci kan yadda matsalar cin hanci da rasahawa ta dabaibaye da yawa daga cikin ma’aikatar tara haraji wanda a halin yanzu an samu fifiko wajen aiwatar da ayukan tara haraji.
Ya kuma bukaci sauran Ma’aikatu da su tashi tsaye wajen mayar da hankali na samar wa jihar kuɗin shiga domin haɓaka ayyukan ci-gaba.
A nasa jawabin, Kwamishinan Ilimi na jihar Hon. Ali Haruna Makoɗa ya karanto batun yadda za’a samar da hanyoyin aiki dan cigaba da samar da tsaro ga al’aumma da kayayyakinsu.
Wasu daga cikin hanyoyin sun hadar da yanayin bada horo ga jami’an gwamnati da mahimmancin haɗa kai don gudanar da aiki bisa gaskiya da amana don ɗaga martabar Jihar Kano.
Bayan haka kuma akwai batun ƙara samar da hanyar da za ta inganta hanyoyin samar da haraji da samar da hanyar da za ta kasance ta haɗa dukkan masu-ruwa-da-tsaki ta hanyar gudanar da ayyuka kafaɗa-da-kafaɗa.
