Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta sa baki a rikicin farashin man fetur da ake yi tsakanin matatar Dangote da kuma kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ba, tare da bayyana cewa an hana kasuwar hada-hadar kuɗi ta man fetur samun sukuni.
Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, ya ce matakin da fadar shugaban aasa ta ɗauka ya yi daidai da dokar masana’antar man fetur da ta bai wa NNPCL cin gashin kai a matsayin wata ƙungiya mai zaman kanta ba.
Onanuga ya fayyace cewa matatar Dangote a matsayinta na kamfani mai zaman kanta tana da haƙƙin ƙayyade farashin man ta.
Mai taimaka wa shugaban kasar ya jaddada cewa tun da aka haramtawa ‘yan wasa irin su matatar man Dangote, suna da ‘yancin sayar da kayayyakinsu a kan ƙayyade farashinsu.
