Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Olayemi Cardoso ya ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arzikin da ake fama da shi a kan rashin tafiyar da tattalin arzikin ƙasa yadda ya kamata tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.
Cardoso ya yi nuni da a wannan lokaci ne a tsakanin wa’adi biyu na mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Gwamnan na CBN ya ce gwamnatin mai ci ta shiga cikin wani mawuyacin hali na samar da kuɗi.
A cewarsa, a cikin shekaru takwas da suka wuce, an sami wani abin ban mamaki da aka yi ta zuba kuɗi a cikin tsarin, dalilin, inji shi, ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki da kuma taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar bakiɗaya.
Gwamnan babban bankin na CBN ya bayyana cewa, a yayin da tattalin arzikin ƙasar ke ƙaruwa da kashi 1.2 cikin ɗari a wancan lokacin, kuɗin kuma ya ƙaru da kashi 12.6 bisa ɗari. Ya kuma ɗora alhakin faɗuwar farashin man fetur da kuma farashin canjin kuɗi kan tsohuwar gwamnati.
Cardoso ya yi imanin cewa, shawarar da babban bankin ƙasar ya yanke na baya-bayan nan, da suka haɗa da kawar da koma bayan musayar kuɗaɗen waje da kuma ƙara tsananta farashin a karo na takwas a cikin shekara guda, na taimakawa wajen dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari kan tattalin arziki.
