Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Alamu sun bayyana cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta saki masu zanga-zangar matsin rayuw da ke tsare a hannun ta.
Majiyoyi a ranar Lahadi sun tabbatar da sakin masu zanga-zangar da aka kama saboda rawar da suka taka a zanga-zangar matsin rayuwa bisa umarnin babban daraktan hukumar DSS, Adeola Ajayi.
Majiyar wadda ta ke da masaniya kan lamarin, ta yi magana kan lamarin, inda ta ce: “Zan iya tabbatar da cewa, Babban Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, a ranar 19 ga Satumba, 2024, ya ba da umarnin a gaggauta sakin masu zanga-zangar da aka kama saboda rawar da suka taka a cikin zanga-zangar #EndBadGoɓernance.
“Waɗanda aka saki sun yaba da wannan karimcin tare da nuna kwarin gwiwa kan irin mutuntakar da aka nuna musu yayin gudanar da binciken.
“Mutane shida da ake tsare da su a Kaduna sun sami ’yanci bayan an wanke su a aarshen bincike. Duk da haka, uku ana ci gaba da tuhumar su .”
Majiyar tsaron ta ci gaba da cewa shugaban DSS ya sake jaddada ‘yancin ɗan ƙasa na gudanar da zanga-zangar lumana kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada da kuma bin doka da oda, duk da haka, hukumar ba za ta bar waɗanda ke fakewa da zanga-zangar ba wajen aikata laifuka.
A cewar majiyar, “Shugaban DSS ya ƙuduri aniyar tabbatar da aikin hukumar na gudanar da bincike mai tsauri tare da gurfanar da waɗanda ke amfani hanayoyin wajen aikata laifuka.”
