Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta kama wani matashi mai shekaru 21 da ake zargi da fasa kabarin maƙabartar Kiristoci ya na sace rodika a Yelwan Kagadama.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Ahmed Muhammed Wakil ya fitar a ranar Lahadi, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
Wakil ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin cewa yana cire rodika daga kaburbura kuma ya siyar da su ga ‘yan gwangwan.
Ya ƙara da cewa, ya na siyar da rodin kan Naira 9, 500 da dubu 12 da kuma Naira 5, 500.
Sanarwar ta ce, “A ranar 20 ga watan Satumba, rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta kama Dauda Saidu, mai shekaru 21 dake zaune a Yelwa bisa zargin sata da lalata kabarurruka.
“Wanda ake tsare da shi, ya shiga maƙabartar Kiristoci a Yelwan Kagadama dake Bauchi inda ya lalata Kaburbura da dama tare da sace rodika da rana tsaka.
“A yayin da yake amsa tambaya, Saidu ya amsa aikata laifukan inda ya tabbatar da cewa ya sace rodika da dama tare da siyar da su ga ‘yan gwangwan.”
Agefe guda kuma, wanda ake zargin ya bayyana cewa yana amfani da kuɗin wajen siyan ganyen wiwi da abinci.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Musa Muhammad ya bada umarnin gurfanar da Saidu da zarar an kammala bincike.
