Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Masu zirga-zirga da matafiya a Kaduna da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna sun yaba wa rundunar sojojin Nijeriya kan daƙile ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a babbar hanyar.
Sun ce harkokin tattalin arziki da kasuwanci na ƙara haɓaka a kan a yankunan babbar hanyar saboda zaman lafiya da aka samu.
Wata sanarwa da Babban Daraktan ‘Ayudantes Empowerment Initiative’ (AEI) Amechi Chuks Oyema ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi, ta ce sun yi wannan yabon ne yayin wani taron wayar da kan jama’a kan zaman lafiya da ci gaban da AEI ta gudanar a ranar Juma’a.
Ya ce ayyukan wayar da kan zaman lafiya da ci gaba ta kai tawagar zuwa unguwar Rigasa, babbar kasuwar Kaduna, Kano Road, Barkin Ruwa bypass da kuma dajin Abuja, duk a Kaduna.
A cewar ƙungiyar, “matafiyan sun yaba wa sojoji a ƙarƙashin babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar Christopha Musa bisa yadda suka matsa wa rayuwar masu aikata laifuka a kan hanyar.
“A lokacin wayar da kan jama’a, masu matafiyan sun yaba wa dakarun soji kan yadda suka daƙile ‘yan ta’adda da suke yunƙurin yin hijira daga dajin Alawa a Jihar Neja zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
“Sun koka da yadda ayyukan ’yan ta’addan ke yim illa a kan hanyar da sauran yankunan jihar, inda ya shafi kasuwanci da ci gaban tattalin arziki.
“Sun yi kira ga sojoji da su tabbatar da cewa sun tsegunta dazuka domin kamo masu garkuwa da mutane da masu haɗa baki da su.
“Sun yi marhabin da gangamin wayar da kan jama’a, inda suka ce wannan mataki ne na samar da goyon baya ga dakarun sojin da ba sa ja da baya wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba a Kaduna kaɗai ba har ma da yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya.
“Har yanzu ƙungiyar samar da zaman lafiya da ci gaba ta ɗauki Ayudantes Empowerment Initiatiɓe zuwa Legas, Keffi da Kaduna.”
