Tsohon Alƙalin alƙalan Gombe ya yi kira da a hanzarta aikin haƙo mai na Kolmani

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Tsohon Alƙalin Alƙalan Jihar Gombe, Mai Shari’a Mu’azu Abdulkadir Pindiga, ya nuna damuwarsa matuƙa game da jinkirin ci gaban aikin haƙo man fetur a rijiyoyin Kolmani da ke masarautar Pindiga a Jihar Gombe da wani ɓangare na Jihar Bauchi.

Yayin da yake magana da manema labarai a Gombe ya bayyana muhimmancin wannan aiki, yana mai kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kammala aikin.

Mai Shari’a Pindiga ya bayyana cewa aikin Kolmani na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, ta hanyar ƙara samun kuɗaɗen shiga da samar da ayyukan yi ga ‘yan ƙasa. Ya ce, “Wannan aikin bai kamata a ɗauke shi da wasa ba,” yana mai jaddada fa’idodin da za su biyo baya da zarar an kammala aikin.

Duk da jinkirin da aka samu, tsohon Alƙalin ya bayyana cewa yana da kyakkyawan fata cewa Shugaba Bola Tinubu zai ci gaba da aiwatar da wannan “babban aiki,” musamman bayan ganawar da Gwamna Inuwa Yahaya ya yi da shugaban ƙasa game da aikin haƙo mai.

A wani batu mai alaƙa da hakan, Mai Shari’a Pindiga ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar Jihar Borno game da mummunar ambaliyar ruwa da ta afka musu kwanan nan. Ya yabawa gwamnatin tarayya bisa bayar da tallafin Naira biliyan uku ga waɗanda lamarin ya shafa, yana mai bayyana wannan a matsayin babbar alama ta kyauta da jinƙai daga shugaban ƙasa.

Har ila yau, ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa su ɗauki matakan da suka dace domin hana faruwar irin wannan bala’i a nan gaba.

By ukarofi