Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kungiyar Editocin Nijeriya (NGE) ta ce za a gudanar da babban taronta na shekara-shekara na bana daga ranar 7 zuwa 9 ga watan Nuwamba, 2024 a garin Yeanagoa na Jihar Bayelsa.
Kungiyar ƙwararrun editoci da shugabannin kafafen yaɗa labarai a Nijeriya, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin ɗin da ta gabata ta bakin shugabanta, Eze Anaba da Babban Sakatare, Dokta Iyobosa Uwugiaren, sun ce taron Editocin Nijeriya (ANEC), wanda za a gudanar, Mataimakin Shugaban Tarayyar Nijeriya Alhaji Kashim Shettima ne zai ƙaddamar da Shugaban kuma Babban Editan jaridar THISDAY da Arise Media Group, Prince Nduka Obaigbena, inda Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ne babban mai masaukin baƙi.
NGE ta ƙara da cewa, tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Segun Osoba da kuma wanda ya kafa jaridar ɓanguard, Uncle Sam Amuka, za su kasance manyan iyaye.
Da suke ƙarin haske kan taron, editocin sun ce tun lokacin da gwamnati mai ci ta hau mulki, a watan Mayun 2023, an shaida irin faɗi-tashin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen ci gaban tattalin arziki domin samar da ci gaba a Nijeriya.
ƙungiyar ta yi kiyasin cewa, yayin da talauci a ƙasar ya kai kusan kashi 40 cikin 100 – inda aka kiyasta cewa ‘yan Nijeriya miliyan 88 ne ke fama da talauci, hauhawar farashin kayayyaki da hauhawar farashin lantarki, ya kasance babbar damuwa ga ’yan Nijeriya da dama.
A cewar NGE, “domin tunkarar waɗannan ƙalubale na tattalin arziki da kuma samun ci gaba, akwai kusan matsaya ɗaya a tsakanin masu ruwa da tsaki cewa ƙasar nan na buƙatar a ɓullo da tsare-tsaren masu fa’ida waɗanda za su tinkari matsalolin ƙasar.
