Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata muhawara mai zafi ta barke tsakanin Gwamnatin Tarayya da ƙungiyar Manyan Dattawan Arewa (NEF) kan batun wani kamfanin tace zinari da ake zargin ana ginawa a jihar Legas, bayan da ƙungiyar ta zargi gwamnati da karya ƙa’idojin adalci da raba albarkatu a ƙasar.
ƙungiyar NEF ta yi wannan zargi ne a cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 18 ga Janairu, 2026, inda ta ce kafa abin da ta kira “Babban Matatar Zinari ta ƙasa” a Legas ba daidai ba ne, ganin cewa mafi yawan ma’adinan zinari da ake haƙowa na Arewa ne.
Wasiƙar, wadda kakakin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere ya sanya wa hannu, an aike ta ne zuwa ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma mambobin majalisar zartarwa ta tarayya.
NEF ta ce matakin da aka ɗauka ya sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulki kan adalci, rarraba arziki da kuma bunƙasar tattalin arziki ga kowa da kowa.
ƙungiyar ta jaddada cewa kafa cibiyar tace zinari a nesa da inda ake haƙar ma’adinan na cire wa Arewa damar ayyukan yi, musayar fasaha da kuma ribar tattalin arziki, tare da ƙara mayar da arziki a hannun Legas da kewaye.
NEF ta ambaci sashe na 14(3), 16(1)(b) da 162(2) na kundin tsarin mulkin 1999, tana mai cewa ƙa’idojin daidaito da rabon albarkatu ya kamata su shafi ba mukamai kaɗai ba, har da wuraren da ake kafa manyan ayyukan tattalin arziki.
ƙungiyar ta ce yadda ake tace zinari a nesa da inda ake haƙarsa wata hanya ce ta tsohon salon mulkin mallaka, inda ake fitar da albarkatu ba tare da anfani ga al’umma ba.
Ta gargaɗi cewa ci gaba da ware Arewa daga irin wannan anfani zai ƙara tsananta talauci, rashin aikin yi, matsalar tsaro da kuma haifar da ƙiyayya tsakanin yankuna.
NEF ta buƙaci a gina a kalla babbar matatar zinari a cikin jihohin Arewa masu arzikin zinari, ciki har da Zamfara, Kebbi, Neja, Kaduna da Katsina, tana mai ba da shawarar a takaita rawar Legas zuwa harkokin kasuwanci, tabbatar da inganci ko fitar da kaya waje.
Sai dai Ma’aikatar Ma’adinai ta Tarayya ta gaggauta mayar da martani, tana kiran zargin na NEF da “rashin sani haɗe da son tayar da fitina.”
A wata sanarwa da mataimakin ministan yaɗa labarai, Segun Tomori ya fitar, an bayyana cewa matatar zinari da ke Legas ba mallakin gwamnati ba ce, illa kamfani mai zaman kansa na Kian Smith, mallakin ‘yan Nijeriya.
Sanarwar ta ce babu wata hujja ko kadan da ke nuna cewa Gwamnatin Tarayya ce ta kafa matatar ko ta zaɓi wurin. Ta kara da cewa gwamnati ba ta da ikon tilasta wa ‘yan kasuwa su gina kamfanoninsu a wani yanki na ƙasa.
Ma’aikatar ta bayyana cewa abin da ministan ma’adinai, Dakta Dele Alake ya faɗa a Saudiyya kawai na nuna fara aiki da wannan kamfani mai zaman kansa a Legas. Haka kuma ya sanar da cewa akwai wasu matatu guda uku da ake gina su a sassa daban-daban na ƙasar, dukkaninsu na kamfanoni masu zaman kansu ne.
Baya ga haka, ministan ya ambaci wasu manyan zuba jari da ake yi, ciki har da masana’antar sarrafa lithium ta dala miliyan 600 da wata ta sarrafa sinadarai masu daraja ta dala miliyan 400 a jihar Nasarawa, da kuma wata ta dala miliyan 200 a Abuja.
Ma’aikatar ta ce, matatar Legas ta nuna nasarar sabon tsarin gwamnati na kara darajar ma’adinai a cikin gida maimakon fitar da su danye. Ta ce wannan tsari ya jawo manyan jari daga ƙasashen waje tare da samar da dubban ayyukan yi.
Har ila yau, ta zargi NEF da rashin yin bincike kafin fitar da sanarwa mai zafi, tana mai gargaɗin cewa irin wannan kalamai na iya tayar da hankula a ƙasa.
Duk da bayanin gwamnatin, ƙungiyar NEF ta ce batun ba mallaka kawai ba ne, illa adalci da daidaito a rarraba damar tattalin arziki. Ta gargaɗi cewa duk yankin da aka hana anfani daga albarkatunsa ba zai zauna lafiya ba har abada, tana mai cewa wannan lamari wata jarrabawa ce ga shugabanci da bin kundin tsarin mulki.
