Daga MUAZU HARDAWA a Damaturu
Kungiyar Muslim Ummah shiyyar Arewa maso Gabas ta fara gudanar da taron masu ruwa da tsaki a garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe, domin tattauna hanyoyin magance matsalolin shugabanci da sauran ƙalubalen da ke addabar al’ummar Musulmi a shiyyar.
An fara taron ne a Cibiyar Musulunci ta Kasa da ke Damaturu a ranar Juma’a 16 ga Janairu, 2026, inda ake sa ran zai gudana na tsawon kwanaki uku, tare da kammala shi a ranar Lahadi 18 ga Janairu, 2026.
A yayin taron, an gayyato shugabannin ƙungiyar Muslim Ummah, mambobin Majalisar Shura, da wakilan wasu kungiyoyin Musulunci domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen fuskantar ƙalubalen da Musulmi ke fuskanta a yankin.
Shugaban ƙungiyar Muslim Ummah na jihar Yobe, Farfesa Muntaka Tanko, shi ne ya buɗe taron a daren Juma’a. A cikin jawabin nasa, ya bayyana muhimmancin taron, inda ya ce zai zama dandalin da za a tattauna manyan matsalolin da ke addabar al’ummar Musulmi, musamman a fannonin ilimi, tsaro, kiwon lafiya da walwalar jama’a gaba ɗaya.
Shi ma shugaban Cibiyar Bunkasa Musulunci ta jihar Yobe, Dakta Injiniya Zaji Bunu, ya gabatar da muhimman sharudda guda goma da aka tsara domin gano matsalolin da kowace jiha ke fuskanta a karkashin ƙungiyar Muslim Ummah, da nufin samar da hanyoyin magance su ta hanyar tsari mai ɗorewa.
A ci gaba da taron, an bayyana cewa za a zaɓi wakili guda daga kowace jiha ta shiyyar Arewa maso Gabas da kuma jihar Jigawa domin kafa wani kwamitin da zai rika tuntuɓar al’umma, tare da hada kai wajen magance matsalolin da suka shafi Musulmi da Musulunci a yankin.
An kuma jaddada muhimmancin dogaro da kai, ta hanyar koyar da sana’o’i, domin taimaka wa Musulmi su fita daga mawuyacin halin talauci da matsin tattalin arziki.
Haka kuma, wakilai daga gwamnatin tarayya sun halarci taron inda suka bayyana yadda za a tsara ayyukan haɗin gwiwa domin cimma sakamako mai kyau.
Shugaban Majalisar Shura ta ƙasa, Barrista Muzammil Sani Hanga, ya yi jawabi kan halin da ake ciki, tare da bayyana yadda ayyukan ƙungiyoyin Musulunci za su iya amfanar da al’umma idan aka gudanar da su cikin tsari da gaskiya.
A madadin shugabannin shiyyar, shugaban Muslim Ummah na jihar Bauchi, Alhaji Umar Ali, ya yi jawabi inda ya buƙaci a ƙara haɗa kai domin ƙarfafa ayyukan ƙungiyar Muslim Ummah a shiyyar Arewa maso Gabas.
A ranar Asabar 17 ga Janairu, 2026, an ci gaba da taron a dakin karatu na Goɓernment Girls College, Damaturu, ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon Ministan Ilimi, Malam Ibrahim Shekarau.
A jawabin da ya gabatar, Shekarau ya ja hankalin shugabanni da daukacin Musulmi da su tashi tsaye wajen bayar da gudunmawa domin gyara matsalolin da suka shafi Musulmi da Musulunci a Nijeriya.
Ya jaddada muhimmancin neman ilimi da tarbiyya ta gari a matsayin ginshiƙin magance matsalolin tsaro, tattalin arziki da zaman lafiya da ƙasar ke fuskanta.
Ya kuma buƙaci mahalarta taron da su sauke nauyin da ke kansu wajen bayar da gudunmawar da za ta taimaka wajen fuskantar ƙalubalen da ke gaba.
A ƙarshe, shugabannin ƙungiyar Muslim Ummah na jihohin shiyyar Arewa maso Gabas sun gabatar da rahotannin ayyukan da ƙungiyarsu ke gudanarwa a jihohinsu, ciki har da tallafa wa al’umma, ayyukan da’awa da ilmantarwa, domin tabbatar da cewa ana tafiya tare a tsira tare.
