
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon ɗan takarar shugaban kuma jagoran Jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ayyana 23 ga watan Junairu a matsayin “ranar butulci” bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya fice daga jam’iyyar akan raɗe-raɗin komawarsa APC mai mulki.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin gabatar da jawabi ga magoya bayansa a Kano jim-kaɗan bayan Gwamna Abba ya bar NNPP a hukumance.
Ya bayyana ranar a matsayin lokaci na dindindin na tuni ga karya alƙawari da butulci a siyasa bisa la’akari da matakin gwamnan, wanda masu sha akan harkokin siyasa suka ayyana a matsayin yaronsa na siyasa.
Tsohon gwamnan na Kano ya ƙara da cewa, ya kirayi gwamnan a keɓance da ya cigaba da zama a jam’iyyar, yana mai ƙalubalantar mayar da ƙarfin jama’a na faɗa-a-ji zuwa ga abokan hamayyar siyasa.
Ficewar Abba Kabir Yusuf daga NNPP ta sanya al’amuran siyasa a Kano sun ɗauki zafi da kuma haddasa cece-kuce acikin magoya bayan jam’iyyar a jihar.
